Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gwamna Dikko Raɗɗa ya sanar da haka lokacin da yake karɓar baƙuncin babban daraktan hukumar bincike da bunƙasa fasahar kimiyyar halitta (NBRDA) ta ƙasa Farfesa Abdullahi Mustapha a gidan gwamnatin jihar.
Ya bayyana matsalolin da ƙananan manoman auduga ke fuskanta na rashin ingantaccen iri.
“Amma duk da wannan matsaloli gwamnati na bakin ƙoƙarin ta wajen dawo da noman auduga da samar da ingantaccen iri ga manoman,”inji Dikko Raɗɗa.
A cewar malam Dikko Raɗɗa gwamnatin jihar ta kashe makudan kuɗaɗe wajen bunƙasa noma ta hanyar samar da kayan noma na zamani.
Ya tabbatar da cewa gwamnati a shirye take ta bada goyon baya wajen ƙulla alaƙa da kamfanin Al-hilal domin kafa cibiyar samar da naman dabbobi a jihar.
A jawabinsa shugaban kamfanin Alhaji Dikko Ladan ya bayyana cewa samar da wannan cibiya a Katsina zai taimaka wajen bunƙasa tattalin arzikin jihar domin za a rinƙa fidda naman zuwa ƙasashen waje.
“Kuma Nijeriya za ta zama ɗaya daga cikin ƙasashen da ke fitar da naman dabbobi zuwa ƙasashen waje,”inji Ladan.
Ya faɗawa gwamnan cewa shi wannan shiri zai taimaka wajen bunƙasa kiwon dabbobi da zai samar da abin yi ga matasa da sauran al’ummar jihar.
Tuna farko babban daraktan hukumar NBRDA wanda ya sami rakiyar shugaban kamfanin Dar_alhilal ya shaida wa gwamnan cewa sun kawo ziyara a jihar ne domin neman haɗin gwiwa da gwamnatin jihar wajen kafa cibiyar sarrafa naman dabbobi a jihar.
Ya ba gwamnan tabbacin cewa ƙulla wannan alaƙa zai taimaka wajen bunƙasa tattalin arzikin jihar,rage talauci da samar da abin yi.
