Tsohon gwamnan Oyo, Ladoja na shirin zama Olubadan na Ibadan bayan rasuwar Olakunlehin

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

A safiyar yau Litinin ne Oba Olakunlehin ya rasu, kwanaki biyu da cikar sa shekaru 90 a duniya.

Lamarin da ya sa ake ganin tsohon gwamnan Jihar Oyo, Rashidi Ladoja ka iya zama wanda zai maye gurbinsa a matsayin sarki, wato Olubadan na Ibadan na gaba.

A ranar 12 ga watan Yulin 2024 ne Gwamman Oyo, Injiniya Seyi Makinde ya naɗa Oba Olakunlehin a matsayin Olubadan na Masarautar Ibadan.

Mutuwar Olakunlehin ta nuna cewa wanda zai gaje shi a kujerar yanzu shine Babban Alƙali, Rashidi Adewolu Ladoja, wanda ɗaya ne daga cikin manyan ƴan sarautar gargajiya na Ibadan.

A matsayinsa na Otun Olubadan, Ladoja shine wanda ke da damar zama sabon Olubadan ɗin duba da yadda dokokin masarautar ta tsara.

A ranar 25 ga watan Satumbar alif 1944 ne aka haifi Rashidi Ladoja, wanda ya zama ɗan siyasa, ɗan kasuwa kuma jagora a sarautar gargajiya.

Ya yi gwamna a Oyo daga shekarar 2003 zuwa 2006, lamarin da ya sa ya zama ɗaya daga cikin tsirarun ƴan siyasar da ke riƙe da muƙaman gargajiya a Nijeriya.

By Babaji