Gwamnatin Kano ta samar da na’urar rarraba hasken wutar lantarki 500

Spread the love

Daga HAMISU IBRAHIM a Kano

A ƙoƙarin gwamnatinsa na samar da hasken wutar lantarki a lunguna da saƙuna na jihar Kano, Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya samar da ƙarin taransfoma 500.

A lokacin da yake ƙaddamar da rabon na’urorin a ma’aikatar samar da lantarki da ke a Maganda Road yace an samo na’urorin ne daga wani kamfani sahihi a ƙasar waje.

A saƙon mai magana da yawun gwamnan Sanusi Bature Dawakin Tofa, Gwamna Yusuf ya nuna matuƙar farinciki da kashin farko na aikin rabon.

“Na tsaya a gabanku cikin alfahari da jin daɗi a ƙaddamar da aikin rabon na’urar taransfoma 500 da za a kai sassa daban-daban a ƙananan hukumomi 44 na jihar Kano.”

A cewar gwamnan wannan wani ɓangare ne na cika alƙawari da gwamnatinsa ta ɗauka musamman ga batun samar da lantarki a yankunan karkara da a tsawon lokaci aka manta da su.

“Samar da lantarki tsayayye ba kawai abin buƙata bane na yau da kullum zai bunƙasa tattalin arziki da masana’antu da inganta lafiya da ilimi da walwalar al’umma baki ɗaya.”

Kazalika, gwamna Yusuf ya bayyana cewa aikin samar da na’urorin lantarkin na haɗin gwiwa ne tsakanin gwamnatin jihar Kano da ƙananan hukumominta.

By ukarofi