Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Cibiyar TBL wadda gwamnatin jihar Katsina ta assasa ta a ƙaramar hukumar Rimi, domin duba masu lalaurar Tarin-Fuka, (Tuberculosis) tun daga matakin awon cutar, bayar da magani, aiki idan ta kama, da sauransu, za su zamo kyauta ga masu ɗauke da cutar, sannan kuma bayar da maganin a gare su, yana ɗaukar makonnin biyu zuwa shida.
Dr. Muktar Aliyu shugaban yaƙi da cutar tarin-fuka ta jihar Katsina, ya bayyana jin daɗin game da ƙaddamar da cibiyar da gwamantin jihar Katsina ta yi, ya ƙara da cewa, samar da cibiyar zai samar ma al’ummar da ke fama da cutar a yankunan Arewa masu Yamma sauƙi, wajen maganceta da kuma hana yaɗuwarta a tsakanin al’umma.
Shugaban karamar hukumar Rimi Alhaji Muhammad Ali Rimi, wanda ya samu wakilcin Hon. Salisu Dahiru Maje ya yi godiya ga gwamnatin Dikko Raɗɗa da ta samar da cibiyar a ƙaramar hukumar, sannan kuma ya bayyana muhimman ayyukan da ƙaramar hukumar tayi ga al’ummar yankin a fannin kiwon lafiya.
Kwamishinan lafiya na jihar Katsina Hon. Musa Adamu Funtua, a yayin jawabinsa wajen taron, ya ja hankalin al’ummar da za su amfana da cibiyar da su zamo masu kishi tare da kiyaye dukiyoyin da aka zuba a ciki, domin tabbatar da ɗorewar cibiyar da kuma amfanuwar al’umma da cibiyar.
Ya ƙara da cewa, gwamantin jihar Katsina ƙarƙashin jagorancin Malam Dikko Umar Raɗɗa, kullum ƙofar ta a buɗe take, domin karɓar ƙorafe-ƙorafen al’umma, da kuma bayar da shawarwari a gare ta, ya ce wannan cibiyar za ta zama abun alfahari ga al’umma, domin an samar da ita ce domin yima majiyancin dake fama da lalurar Tarin-Fuka komi a kyauta, ba tare da kashe ko sisi ba.
