DSS ta kama ɗan TikTok, Waspapping a Kaduna kan yaƙin Amurka/Isra’ila da Iran

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Hukumar Tsaro ta Farin kaya DSS, ta kama wani mai sharhi a kafafen sada zumunta mai suna Sani Waspapping, wanda ake kira “Sarki” a dandalin X.

Rahotanni sun ce an kama shi ne a yammacin ranar Juma’a a kusa da NEPA Roundabout a birnin Kaduna. Saidai ba a bayyana takamaiman zargin da ake yi masa ba.

Wasu abokansa sun ce an kama shi ne saboda ra’ayoyin da ya bayyana kan yaƙin tsakanin Amurka da Isra’ila a gefe guda da kuma Iran a ɗaya ɓangaren.

Rahoton ya ce an kama shi tare da wani abokinsa, saidai daga bisani an saki abokin, lamarin ya sa abokai da magoya bayansa suka fara kiraye-kirayen a sake shi.

Har zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoton, ba a san inda ake tsare da shi ba, kuma ana shirin tattara lauyoyi domin neman bayani daga DSS game da dalilin tsare shi.

By Babaji