Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
A wata hira da manema labarai Shehu Usman Dalhatu Karkarku wanda yayi magana a madadin ‘yan uwa mabiya Sayyid Ibrahim Zakzaky ya zargi jami’an sojoji da ‘yan sanda da bibiyar su a yayin da suke gudanar da muzahara.
Yace suna gudanar da muzahara ne domin nuna jimami, juyayi da damuwa kan kisan da aka yiwa Sayyid Ali Khamene’i da ƙasashen Amurka da Isra’ila suka aiwatar.
“Sai muka ga gamayyar jami’an tsaron sojoji da ‘yan sanda ɗauke da muggan makamai a motocin yaƙi masu sulke suna sintiri a cikin garin Katsina tun tsawon mako guda,”inji Dalhatu karƙarku.
Ya bayyana cewa fiye da shekara 30 tun lokacin mulkin soja suke gudanar da muzahara cikin lumana,”Ba a taɓa tada hankali ba,” ya ce.
Saboda haka ya jawo hankalin gwamna Dikko Raɗɗa da duk masu faɗa aji a jihar da sauran jama’a cewa,suka ga wani abu ya faru a cikin al’umma to su tuhumi jami’an tsaro da suka zaƙu don su shekar da jinin al’umma.
Karkarku ya bayyana cewa duk a ƙasashen duniya ana ta gudanar da irin wannan nuzahara amma sai a
nan Nijeriya ake take wannan yancin da tsarin mulki ya bada damar ayi.
Al’ummar jihar Katsina su shaida idan ‘wani abu ya faru a yanzu daga jami’an tsaro ne,”Inji karkarku.
