Gwamnatin Katsina ta ɗauki matakin bunƙasa noman mangwaro a faɗin jihar

Daga UMAR GARBA a Katsina

Gwamnatin Jihar Katsina ƙarƙashin jagorancin Aminu Bello Masari, ta ɗauki matakin bunƙasa ayyukan noman mangwaro a faɗin Jihar Katsina.

Shugaban ƙungiyar masu noma da sarrafa mangwaro, ya ce an shirya horon ne domin a ƙarfafa guiwa tsakanin manoman mangwaro don inganta samar da kuɗaɗen shiga a jihar Katsina.

Alhaji Abdulkadir Mamman Nasir M.D na hukumar KATARDA, wanda ya samu wakilcin Alhaji Abubakar Dabo, ya bayyana cewa, taron zai taimaka matuqa ga mahalartan domin su samu ilimi na yadda ake dasa gami da rainon itatuwan mangwaro ya zuwa girmansu a zamanance.

Ya ce hakan zai taimaka wajen tafiya kafaɗa da kafaɗa wajen samun riba gami da samar da ayyukan yi ga al’umma.

Mai bai wa Gwamna Shawara na Musamman, Abdulkadir Nasir, ya ce fiye da mutane 100 ne aka zaɓo a sassan.

Katsina aka koyar da su ilimin dashen mangwaro, kamar yadda Katsina Post ta rawaito.

Alhaji Abdulkadir Mamman Nasir ya yi nuni da cewa, bincike ya bayyana cewa itatuwan mangwaro guda 3 za su iya ɗaukar ɗawainiyar yaro a wajen karatunsa tun daga makarantar firamare har zuwa makarantar koyan ilimi mai zurfi.

A dalilin haka ne ya ƙara bayyana cewa, noman mangwaro wata hanya ce ta samun kuɗaɗen shiga gami da inganta tattalin arziki, ya ce waɗanda suke amfana da wannan horo sun haɗa da; Masu duba yadda ake gudanar da shirin samar da tallafin na musamman da masu amfana da shirin samar da tallafin kuɗi mai sharaɗi da ƙungiyar manoma ta matakin farko da masu amfana da shirin N-Power da kuma masu dafa abinci na makarantun firamare da sauransu.