Ka yi kaɗan ka rushe sabbin masarautun Jihar Kano – Ganduje ga Abba Gida-Gida

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

A ranar Talata ne gwamnatin jihar Kano ta shaida wa jam’iyyar adawa ta New Nigeria People’s Party, NNPP cewa shirinta na mayar da tsohon birnin ga tsohon masarautu tare da kakkave sabbin masarautu ba zai tava yiwuwa ba.

Gwamnatin ta ce sabunta sheqar da ɗan takarar gwamna na Jam’iyyar NNPP, Abba Kabir Yusuf ya yi na sallamar sabbin masarautu idan aka zaɓe shi, hakan na nufin ba zai yi aiki da dokar kafa sabuwar masarautu da kuma shawarar da jama’a suka yanke.

Gwamna Ganduje ta bakin Kwamishinan yaɗa labarai da harkokin cikin gida na jihar, Muhammad Garba, a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai ya ce an bi tsarin da ya dace ta hanyar samar da dokoki da majalisar dokokin jihar ta yi, waɗanda kuma dole sai an yi watsi da su kafin rufe masarautun.

Garba ya yi nuni da cewa, kamar yadda aka kafa jihohi da qananan hukumomi, sabbin masarautu na ƙara wa jihar ci gaba a matsayin masu ruwa da tsaki saboda dokokin da suka kafa su sun bayyana ayyukansu a fili.

Kwamishinan ya bayyana cewa samar da sabbin wuraren da aka daɗe ba a yi ba, ya kawo ci gaban zahiri, zamantakewa da al’adu da ba a tava ganin irinsa ba a yankunan.

Ya ƙara da cewa, sabbin masarautun da ke samun cikakken goyon bayan jama’a, sun fi yin allurar wasu kamanceceniya da jama’a ke shiga cikin harkokinsu na ci gaban tattalin arzikinsu ta hanyar cibiyoyin gargajiya.

Kwamishinan ya kuma bayyana cewa, samar da masarautu na daga cikin ƙudirin gwamnati na tallafa wa ci gaban kananan garuruwa domin ganin an samu nasarar Kano a matsayin babban birnin.