Direbobin tanka sun toshe hanyar Zariya-Kano bayan kashe abokin aikinsu

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Direbobin tanka sun toshe babbar hanyar Zariya zuwa Kano a ranar Laraba don nuna tsantsan vacin ransu kan kashe ɗaya daga cikinsu da wani soja ya yi.

Lamarin ya faru ne wajen misalin ƙarfe 3:30 na yamma, lokacin da direbobin suka haddasa mummunan cunkoson ababen hawa sakamakon rufe hanyar na tsawon sa’o’i.

Ba a gano asalin abin da ya kai har sojan, wanda ke aiki tare da wani kamfanin gine-gine, ya kashe direban ba. Sai dai bayanai sun nuna lamarin ya faru ne a kusa da garin Tashar Yari da ke Ƙaramar Hukumar Makarfi ta Jihar Kaduna.

Da ya ke tabbatar da tare hanyar, da ma kisan direban, mai riƙon muƙamin Kwamandan Hukumar Kiyaye Haɗɗura ta Ƙasa (FRSC) reshen Jihar Kaduna, Lawal Garba, ya ce, sai da aka yi amfani da sauran jami’an tsaro kafin a bu&e hanyar ga sauran masu wucewa.

Ya ce, “Toshe hanyar ya fara ne bayan wani soja da ke aiki da kamfanin da ke aikin gina titi ya bundige wani direba saboda wata gardama da ta afku a tsakaninsu.

“Hakan ce ta sa direbobin tankar suka toshe hanyar baki ɗaya don nuna fushinsu.

“Na kira Daraktan DSS da Kwamishinan ’Yan Sanda da kuma Daraktan Tsaron Cikin Gida a kan lamarin. Yanzu haka muna ƙoƙarin shawo kan lamarin,” inji shi.

Tuni dai sojan ake tuhuma da aika-aikar ya faɗa hannun sojoji.

Da aka tuntuɓi Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna, DSP Mohammed Jalige, ya ce tuni Kwamishinan ’Yan Sanda na Jihar, Yekini Ayoku, ya ba da umarnin zurfafa bincike a kan lamarin.