Darajojin Ahlul Baiti a cikin hadisai

Daga MUHAMMED BALA GARBA

Akwai Hadisai da dama da suka yi magana a kan martabobi da darajojin Ahlul Baiti. Za mu takaita kan wasu hadissai ingantattu guda bakwai (7). Amma bari mu soma da waɗannan guda biyu waɗanda suke bayyana fifikon dangin Annabi (Sallalahu Alaihi Wasallam) baki ɗaya akan sauran mutane.

Tirmizi ya rawaito falalar Annabi (Sallalahu Alaihi Wasallam) cewa: Abbas (Allah ya ƙara masa yarda) ya ce: “Na ce wa Manzon Allah (Sallalahu Alaihi Wasallam), Ƙuraishawa sun zauna suna bitar tarihin gidansu. Sai suka kwatantaka da muruccin kan dutse. Sai Annabi (Sallalahu Alaihi Wasallam) ya ce: “Da Allah ya tashi samar da halitta, sai ya zabi mafi alherinta ya sanyo ni a ciki. Ya kuma zabi mafi alherin ƙabilu ya sanyo ni a ciki. Ya kuma zabi mafi alherin gidaje ya sanyo ni a ciki. Saboda haka ni ne mafi alherinsu ga tushe da asali”. Hadisi na biyu da ya da ɗa fitowa da manufar a fili, shi ne:

Imamul Muslimu ya ruwaito daga Wasilatu dan Aska’u wanda ya ce: “Na ji Manzon Allah (Sallalahu Alaihi Wasallam) na cewa: “Haƙiƙa Allah ya zaɓi kinanata daga cikin ‘ya’yan Isma’il. Daga cikin Ƙuraishawa kuma ya zaɓi Banu Hashim. Daga cikin Banu Hashim kuma ya zave ni”. Muna iya lura daga wadannan hadisai guda biyu cewa, Manzon Allah (Sallalahu Alaihi Wasallam) an zabo shine daga dangi zababbbu.

Don haka, duk wanda ya ke tunanin ya san darajar Manzon Allah (Sallalahu Alaihi Wasallam) amma bai san darajar danginsa ba, to bai gano asalin Manzon Allah ba. Haka kuma za mu iya lura cewa, Manzon Allah (Sallalahu Alaihi Wasallam) ya na kula da zumunci na kusa da na nesa, ya na yi mu su addu’a, kuma ya na yi wa musulmai wasicci da su kaunace su, su kula masa da su, su kyautata a matsayin wani haƙƙinsa a kan su. Mu duba wannan hadisi:

Imamul Hakimu ya rawaito a cikin Almustadrak, Imamul Zahabi ya inganta ruwayar daga Hadisin Abdullahi dan Abbas (Allah ya ƙara masa yarda) cewa, Manzon Allah (Sallalahu Alaihi Wasallam) ya ce: “Ya ku Bani Abdul Muddalib, ku sani na rokar muku Allah abubuwa guda Uku:

1- Allah ya tabbatar da duga-dugan waɗanda ke tsaye daga cikinku.
2- Ya kuma shiryar da waɗanda sukayi batan kai daga cikinku.
3- Ya kuma sanar da jahilanku.

Na kuma roke shi ya sanya ku masu tsananin alheri da juriya da jinkai. Kuma lallai da wani mutum zai yi Sallah a tsakanin Rukunin Hajarul Aswad da Al Makam (Makamu Ibrahim), yana kuma dauke da azumi, idan ya mutu ya na kin iyalan Muhammadu, to makomarsa ita ce wuta.” Game da dangi na kusa kenan. To, game da na nesa kuma, mu karanta wannan hadisi:

Imamul Muslim ya rawaito hadisi daga Abu Zar (Allah ya ƙara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (Sallalahu Alaihi Wasallam) ya ce: “Lalle ne za ku ci kasar da ake kira Misra, sunan kudinsu Qirat. Idan kuka ci garin to, ku kyautata wa mutanensa, domin su na da alkawari (akanku) da zumunta. Ko kuma ya ce, alkawari da surukuta a wata ruwaya.

Imamul Nawawi ya fayyace mana wannan wasiyya a in da ya ke cewa, Malamai sun ce: Zumuntar misrawa ita ce, auren da kakan Manzon Allah (Sallalahu Alaihi Wasallam), Annabi Ibrahimu (Allah ya ƙara masa yarda) ya yi da ‘yar garinsu Hajara. Surukuta kuwa ita ce, kasancewar mahaifiyar Ibrahimu dan autan Manzon Allah (Sallalahu Alaihi Wasallam) bamisriya ce.

Sai mu je zuwa ga wasiccin Manzon Allah (Sallalahu Alaihi Wasallam) game da danginsa mafi kusanci Ahlul Baiti. Domin Karin bayani sai a duba: Al Mustadrak, na Hakim, Kitabu “Ma’arifatis Sahabah”, babin darajojin Iyalan Annabi (Sallalahu Alaihi Wasallam) (3/149-148). 21 Sahihu Muslim, Kitabu Fada’il ashabin nabiy, Hadisi na 2543.

A cikin Sahihul Muslim, Zaidu dan Arkamu ya rawaito cewa, Manzon Allah (Sallalahu Alaihi Wasallam) ya faɗa a cikin wata hudubar da ya yi a dai-dai wani tafki da ake kira Gadir Khum.
“Bayan haka, ku sani ya ku mutane, haƙiƙa ni mutum ne Manzon Ubangijina ya kusa ya zo mini in amsa masa (Yana nufin mutuwa).

Zan bar amanar wasu abubuwa guda biyu a hannunku. Na farko shi ne littafin Allah, a cikinsa akwai shiriya da haske, kuyi riko da littafin Allah riko na sosai.” Ya yi matuƙar jan hankalin mutane zuwa ga littafin Allah. Sannan ya ce: “Da kuma Iyalan Gidana, ku riƙe su matsayin amanar Allah, ku rike su matsayin amanar Allah.” Wannan hadisin ya shahara da sunan hadisin Gadir. Kuma ingantacce ne a wurin malaman Sunnah. Yana kuma ɗaya daga cikin hujjojin Ahlul Sunnah na darajanta Iyalan Manzon Allah (Sallalahu Alaihi Wasallam). Duba: Riyadus Salihin, na Nawawi, tare da sharhinsa mai suna Nuzhatul Muttaƙin (1/368).

A cikin Sahihul Muslim, hadisi yazo a cikin fadin Falalar Annabi (Sallalahu Alaihi Wasallam) daga Safiyyatu ‘yar shaibatu, ta ce: Uwar muminai Nana Aisha (Allah ya ƙara mata yarda) ta ce: “Wata rana Annabi (Sallalahu Alaihi Wasallam) ya fita da hantsi yana sanye da wani bakin mayafi mai kauri, sai ga Hassan dan Ali, sai ya sa shi cikin mayafin.

“Sai kuma ga Hussaini, shi ma ya saka shi. Sai kuma ga Fadimatu, ita ma ya saka ta, sai kuma ga Ali, shi ma ya saka shi.” Sannan ya karanta ayar da take cewa: “Allah na nufin ne kawai ya tafiyar da kazanta daga gare ku, ya Ahlul Baiti (Mutanen Babban Gida!) kuma ya tsarkake ku tsarkakewa.” [Suratur Ahzab, aya ya 33]. Duba Sahihu Muslim, Hadisi na 2424.

Imamul Hakimu ya ruwaito hadisi daga Abu Sa’id (Allah ya ƙara masa yarda) cewa, Manzon Allah (Sallalahu Alaihi Wasallam) ya ce: “Na rantse da wanda rayuwata ke hannunsa, duk wanda ke kiyayya da ɗaya daga cikin Ahlul Baiti (‘Yan gidan Annabta), wuta Allah zai sa shi. Duba Al Mustadrak, na Hakim. Kitabu Ma’arifatis Sahabah, Fadi darajojin Iyalan Annabi (Sallalahu Alaihi Wasallam) (3/150).