Gwamnatin Katsina ta ɗauki sabbin malamai 250

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Ma’aikatar Ilimin Firamare da Sakandare ta miƙa takardun kama aiki ga sabbin malamai da ma’aikatan gudanarwa, tare da takardun ɗaukar ɗalibai ga waɗanda aka ɗauka a sabbin makarantun sakandare (Model Secondary Schools) da ke Raɗɗa, Dumurkul da Jikamshi.

Da yake jawabi a wajen taron, kwamishinan ilimin firamare da sakandare, Hon. Yusuf Sulaiman Jibia,
ya buƙaci sabbin ma’aikatan da su nuna ƙwarewa, ladabi, jajircewa da bin ƙa’idojin aiki.

Ya jaddada cewa an ɗauki ma’aikatan ne bisa cancanta, kuma an kafa makarantun domin zama cibiyoyin koyi da ingantaccen ilimi ga sauran makarantun gwamnati a faɗin jihar.

Kwamishinan ya ƙara bayyana cewa an zaɓo ɗaliban da aka ɗauka ne daga makarantun gwamnati na mazabu siyasa 361 na jihar, abin da ke nuna adalci, daidaito da bai wa kowa damar samun ilimi ba tare da la’akari da inda ya fito ba. Haka kuma, ya tabbatar da ƙudurin gwamnatin jihar na farfaɗo da ɓangaren ilimi, inda ya bayyana cewa kasafin kuɗin shekarar 2026 ya tanadi gyaran makarantun sakandare manya da ƙanana guda 74, tare da sauran shirye-shiryen inganta kayan more rayuwa da sakamakon karatu.

A jawabinta, Hajiya Zainab Bugaje daga kamfanin Hallmark Consultancy ta bayyana kafa makarantun koyi a matsayin hangen nesan Gwamna na samar da makarantu na musamman da suka dace da zamani. Ta bayyana cewa an bi hanyoyi masu tsari da tsauri wajen zaɓen malamai da dalibai ta hanyar jarrabawar shiga makarantun.

A nasa ɓangaren, Shugaban hukumar kula da malamai (TSB), Alhaji Sada Ibrahim (Chigarin Dutsinma), ya buƙaci sabbin malamai da su yi aiki tuƙuru domin cimma burin gwamnatin jihar, tare da tabbatar musu da cikakken goyon bayan hukumar.

A madadin al’ummar Raɗɗa, Maigarin Raɗɗa, Alhaji Kabir Umar Bare-Bari, ya gode wa Gwamnan Jihar bisa kafa makarantar sakandare ta musamman a garin Radda, inda ya bayyana shirin a matsayin abin alfahari ga al’umma garin da kewaye.

Shima da yake jawabi, shugaban makarantar ta Raɗɗa, Dr. Lawal Shehu, ya bayyana taron a matsayin wani muhimmin tarihi a ɓangaren ilimi da aikin gwamnati a jihar, inda ya bayyana cewa sama da ma’aikata 250 ne aka ba su takardun ɗaukar aiki a sabbin makarantun. Ya tabbatar da aniyar ma’aikatan wajen riƙe amanar da aka ɗora musu tare da samar da sakamako mai kyau a harkar koyo da koyarwa.

By ukarofi