Shugaban ƙungiyar ‘yan jarida a Katsina ya zama babban sakatare

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Gwamna Dikko Raɗɗa ya amince da naɗin malam Tukur Ɗan Ali daga ƙaramar hukumar Ɗanmusa kuma shugaban ƙungiyar ‘yan jarida ta ƙasa reshen jihar Katsina a matsayin babban sakatare tare da wasu mutane biyu.

A wata takardar sanar wa ɗauke da sa hannun shugaban ma’aikatan jihar Alhaji Falalu Bakake, sauran sun haɗa da Junaidu Muntari da Yahaya Abdullahi daga ƙananan hukumomin Ƙanƙara da Safana.

Ya ce naɗin nasu an yi sh8 ne bisa cancanta inda ya ƙara da cewa sai da suka da suka sami nasarar zama jarabawar da makarantar Civil service institute ta shirya a madadin gwamnatin jihar Katsina.

Bawale ya bayyana cewa matakan da gwamnatin jihar ta ɗauka wajen basu wannan muƙami na mayan sakatarorin ya nuna ƙoƙarin gwamnati wajen amfani da ƙwarewa da cancanta a aikin gwamnati.

Shugaban ma’aikatan ya ƙalubalanci manyan sakatarorin da su bada ta su gudunmawa wajen sabon ƙudirin gwamnati na ‘Gina Makoma,ganin yadda matsayin su yake cikin al’umma.

Ya buƙaci manyan sakatarorin da su fuskanci nauyin da aka ɗora masu ta hanyar nuna juriya da ƙwarewa wajen tafiyar da harkokin gwamnati.

By ukarofi