Da Ɗumi-Ɗumi: Kotu ta bada belin Malami, matarsa da ɗansa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Wata Babbar Kotun Tarayya da ke abin, ta bada belin Naira biliyan 1.5 akan tsohon Antoni-Janar na ƙasa kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami, matarsa, Asabe Bashir da ɗansa, Abdulaziz Malami.

A shari’ar da ta yi a yau Laraba ƙarƙashin jagorancin Alƙali Emeka Nwite, kotun ta bada belin kowane ɗaya daga cikinsu ne akan Naira miliyan 5 bayan Hukumar Hana yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta’annati (EFCC) ta shigar da su ƙara na zargin su da hannu a sauya akalar Naira miliyan 8.7.

Mai Shari’ar ya kuma sanya musu sharaɗin samar da mutane biyu-biyu a matsayin waɗanda za su tsaya musu, waɗanda suke da filaye a Asokoro, Maitama ko kuma Gwarimpa, wato unguwannin birnin tarayyar.

A cewar kotun, bayan miƙa takardun kadarorin domin tantancewa, mutane ukun sai sun kuma bada fasfon tafiye-tafiyensu ga kotun.

Sannan, wajibi ne masu tsaya musun su miƙa wa kotu hotunan fasfo na kwanan nan guda biyu-biyu da takardar shaida akansu.

Haka kuma, kotun ta yi gargaɗin kada kowane ɗaya daga cikin waɗanda ake ƙarar ya yi tafiya zuwa ƙasar waje ba tare da izininta ba.

A yanzu haka dai Malami da sauran biyun za su cigaba da zama a gidan yari har sai an cika sharuɗɗan belin.

A ƙarshe, Alƙalin ya ɗage sauraron shari’ar zuwa ranar 17 ga watan Fabarairu domin sake zama a kai.

By Babaji