
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Tsohon shugaban ƙasa Goodluck Ebele Jonathan, ya bayyana gamsuwa da cewa babbar jam’iyyar adawa (PDP) tana nan da kwarjini da ƙarfinta saɓanin jita-jitar wasu gidajen jaridu, yana ma cewa har yanzu ita ce ginshiƙin dimukraɗiyyar Nijeriya, wadda ta rage daga jam’iyyun da aka kafa a 1998.
Jonathan ya bayyana haka ne a lokacin da ya karɓi baƙoncin mambobin kwamitin gudanarwar (NWC) jam’iyyar na ƙasa ƙarƙashin jagorancin Dakta Kabiru Tanimu Turaki a ofishinsa da ke Abuja a yammacin Talata.
A yayin ganawar, an mayar da hankali ne wajen hanyoyin da suka dace a bi don shawo kan matsalolin ‘ya’yan jam’iyyar da dabarun saita al’amuranta na shirin tunkarar babban zaɓen 2027.
Tsohon shugaban ƙasar ya ce, PDP tana da tarihi mai ban ƙaye wajen ƙarfafa cibiyoyi da ake buƙatarsu yayin fuskantar ƙalubalen cikin gida, inda ya bayyana ta a matsayin cibiyar ƙasa.
Ya kuma yi kira ga jagororin PDP da su fifita maslahar ƙasa da cigabanta sama da ta karan kansu, inda ya ce jam’iyyu masu ƙarfi suna da muhimmanci ga ɗorewar dimukraɗiyya.
A nasa jawabinsa, Dakta Turaki ya yi godiya ga tsohon shugaban ganin yadda ya yi amfani da damarsa ta kasancewarsa uba wajen nasihantar su da biyayyarsa ta gaskiya ga jam’iyyar.
Turaki ya kuma tabbatar masa da cewa jagorancin yanzu ya duƙufa wajen sabunta harkokin jam’iyyar da manufar sake ginawa da ƙarfafa ta.
Waɗanda suks halarci zaman sun haɗa da; Dr. Mu’azu Babangida Aliyu, Farfesa Jerry Gana, Janar Ishaya Bamaiyi, Hajiya Zainab Maina, Cif Mike Oghiadome, Mohammed Bello Adoke, da sauran mambobin NWC.
PDP na fama da matsalolin rikicin cikin gida, wanda hakan ya sa aka samu ‘yan ɓangaren Turaki da kuma na Ministan Abuja Nyesom Wike, waɗanda ke rikici akan shugabancinta.



