Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Majalisar zartaswa ta Jihar Katsina ta amince da bayar da kwangilar gyara hanyar da ta tashi daga Shargalle, Dutsi, zuwa ƙaramar Hukumar Ingawa a zamanta karo na 11 ƙarƙashin jagoranci gwamnan jihar Malam Dikko Umaru Radda ta amince da bada kwangilar gyaran hanyar da ma wasu muhimman ayyukan raya ƙasa.
Da yake shaida wa manema labarai haka bayan kammala taron, kwamishinan ayyuka na jihar Engr. Sani Magaji Ingawa, ya ce “majalisar ta amince da gyaran hanyar mai tsawon kilo mita 39 akan kuɗi sama da Naira biliyan 13.8,” ya ce.
Kwamishinan ya bayyana wannan shi ne gyara na farko da za a yi wa hanyar shekaru ashirin da suka gabata, ya bayyana cewa za a kammala aikin cikin watanni sha huɗu.
Kwamishinan ya kuma bayyana cewa majalisar ta amince da ƙarasa wani tsohon ginin ɗakin karatu da aka fara ba a ƙarasa ba shekaru da dama da suka gabata.