Sakacin likitoci ya sa ‘yarmu ta mutu bayan tiyatar haihuwa – Fatima Widi

Daga UMAR AKILU MAJERI a Dutse

An soki lamirin likitoci dake aiki a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Gwamnatin Tarayya dake Dutse wato Federal Uniɓersity Teaching Hospital Rasheed Shikoni akan sakacin ma’aikatan lafiyar da hakan ya sa ake samun mace-macen mata masu haihuwa. 

Hajiya Fatima Widi Jalo, tsohuwar ‘yar jarida ce da ta yi fice a kafafen yaɗa labarai kuma ta yi aiki a gidajen rediyo daban-daban ciki har da gidan rediyon Jihar Jigawa kuma ta taɓa zama Kwamashiniyar Mata da Walwalar Jama’a ta Jihar Jigawa lokacin mulkin Sule Lamido.

Hajiya Fatima Widi ita ce ta gabatar da ƙorafin cewar sakacin ma’,aikatan lafiya a Asibitin Koyarwa na Shikoni ya yi sanadin mutuwar ‘yar su mai suna Fatima Alfa Umar bayan an yi mata tiyatar haihuwar ‘ya’ya biyu a asibitin “shi ne ma’aikatan lafiya suka yi watsi da ita aka ƙi ba ta kulawar da take buƙata.”

Jalo ta ce sakamakon haka ne ya sa ‘yar tasu ta rasu, ta mutu sakamakon zubar jini da take yi babu ƙaƙƙautawa tana jelen zuwa banɗaki daga gadon da aka kwantar da ita. Jalo ta ce ta lura sosai marigayiyar tana zubar da jini ‘kuma ga shi an sa mata jini kuma jinin ba ya tafiya wanda haka ya biyo bayan sakacin da ma’aikatan jinyar suka yi na gazawar ba ta kulawar da ya kamata a bata.’

Widi ta ce a ranar da Fatima Alfa Umar ta rasu mata huɗu ne suka mutu banda marigayiyar, ta ce wannan kaɗai ya nuna akwai sakaci a ɓangaren masu kula da lafiyar waɗanda aka yi wa aikin tiyatar haihuwa, “don haka akwai buƙatar gwamnati da hukumar lafiya da hukumar gudanarwa ta asibitin na Shikoni ta ɗauki matakin da ya kamata domin ganin duk waɗanda suke da hannu wajen mutuwar matan da suka mutu a a sibitin a ranar 24 ga Oktoba, 2024 ya zama izina ga sauran ma’aikatan lafiya.”

Ta ce ƙin daukar matakin ladaftarwa akan ma’aikatan lafiyar tamkar an kashe maciji ne ba a sare kai ba, saboda haka ya zama dole gwamnati ta ɗauki matakin da zai hana ma’aikatan lafiya wulaƙanta mata masu haihuwa a dukkan asibitoci dake jihar.

Kamar yadda bincike ya nuna ba wai matsalar wulaƙanta marasa lafiya ne kawai ba, akwai ƙarancin wutar lantarki a asibitin duk da maƙudan kuɗi da gwamnati ta kashe wajen wadata asibitin da wutar sola, lamarin da ya tilasta hukumar gudanarwa ta asibitin yin amfani da janareta wajen samar da hasken wutar lantarki a asibitin domin a bai wa ɓangaren sola samar zukar caji daga hasken rana saboda a sami hasken wuta a asibitin cikin dare.

Duk da haka wutar ba ko’ina ne ake samunta ba idan dare ya yi a asibitin duba da yadda Nijeriya ta fada cikin matsalar rashin wuta a lokacin. 

Kamar yadda bincike ya nuna akwai ƙarancin likitoci a jihar ta Jigawa wanda hakan ya biyo bayan rashin albashi mai kyau da likitocin suke fuskanta tun bayan ƙarewar mulkin gwamnatin Sule Lamido har zuwa ƙarshen mulkin gwamnatin Badaru wadda ta miƙa mulki ga gwamnati mai ci.

Haka ya sa ma’aikatan lafiya da dama da manyan likitocin da suke aiki a jihar suka ƙaurace zuwa wasu maƙotan jihohi inda suke samun kulawar da suke buƙata. 

Hajiya Fatima Widi ta buƙaci gwamnatin Jihar Jigawa da ta ɗauki matakin da ya dace kuma ta kafa wani kwamati da zai binciki sanadin mutuwar matan guda biyar a rana ɗaya a asibitin na Shikoni dake Unguwar ɗan Masara, ta ce ita fa ba za ta yi shiru ba akan wannan magana domin sune suke yi wa mata kanfen akan zuwa asibiti awo da haihuwa kuma rashin ɗaukar mataki akan wannan al’amarin tamkar wata tufka ce da warwara. 

Ta ci gaba da cewa za ta nemi haƙƙin ‘yarsu wato Fatima Alfa domin sakacin ma’aikatan lafiya ne ya sa suka rasata, “don haka akwai buƙatar gwamnati ta shiga maganar a zurfafa  bincike a ga waɗanda suke da laifi a hukuntasu.”

Da yake mayar da jawabi a madadin hukumar asibitin Dr Jibrin Abdullahi wanda shi ne likitan da ya yi wa Fatima Alfa Umar aiki, ya ce shi dai a iyaka saninsa lafiya ƙalau suka fito da Fatima Alfa Umar daga ɗakin tiyata kuma aka kwantar da ita a ɗakin hutawa aka kwantar da ita bisa kulawar ma’aikatan lafiya masu kula da marasa lafiya wato Nurses. 

Ya ƙara da cewar “kuma maganar cewar Fatima tana zubar da jini wannan ai ba sabon abu ba ne, idan an yi wa mace mai haihuwa tiyata aikin ciki dole ne jini ya zuba domin jinin biki ne, haka zalika idan ma akwai wani laifi su waɗanda suke zaune a wajenta wato Fatima Alfa sune masu laifi domin sun ba ta abinci kafin lokacin da likita ya ba su ya ce a bata abinci sune ba su bi ƙa’ida ba.”  

Ya ce abinda zai iya tunawa da suka ba ta abinci ta fara yin tari kuma numfashinta ya yi sama ta shaƙe, ya ƙara da cewar ya yi iyakacin bakin ƙoƙarinsa wajen gano dalilin shaƙewar lumfashinta amma hakan ya ci tura daga ƙarshe dai Fatima Alfa Umar ta rasu.

Ya ƙara da cewar: “Mu Musulmi ne kuma duk Musulmi yasan kowanne ɗan Adam mamaci ne kamar yadda Manzon Allah ya faɗa babu wanda ya isa ya kashe ko rayarwa sai Allah, Allah dai ya yi wa Fatima rasuwa amma ba mu ne sanadi ba, domin mu lafiya muka kammala aikinmu muka turata ɗakin hutu.”