Gwamna Sule ya hori zaɓaɓɓun ciyamomin Nasarawa su kasance masu kwatanta gaskiya da amana

Spread the love

Daga JOHN D. WADA a Lafiya

Gwmnan Jihar Nasarawa Injiniya Abdullahi Sule ya buƙaci duka sabbin zaɓaɓɓun shugabannin ƙananan hukumonin jihar da aka zaɓa a ƙarshen makon da ya gabata su kasance masu nuna gaskiya da riƙon amana a yayin da suke gudanar da shugabancinsu.

Duka sabbin shugabannin ƙananan hukumomin 13 waɗanda ‘yan jam’iyyar APC mai ci a jihar ne gwamnan ya ƙalubalance su ne jim kaɗan bayan ya rantsar da su a Lafiya fadar gwamnatin jihar a makon da ake ciki. 

Ya buƙacesu su kuma tabbatar suna aiwatar da ingantattun ayyuka da tsare-tsare da za su kawo canji a yankunan karkara wa al’ummarsu bakiɗaya.

Gwamna Abdullahi Sule ya kuma bayyana zaɓukan wanda duka ‘yan takarar jam’iyyarsa APC mai ci ta lashe inda ta rasa kujeru 7 kacal na kansuloli ga jam’iyyun adawa a matsayin ingantaccen zaɓe wanda a cewarsa aka gudanar banda maguɗi kana ya jinjina wa ƙoƙarin hukumar zaɓukan jihar dangane da aiki tuƙuru da suka yi.

Har ila yau gwamnan ya kuma gode wa sarakunan gargajiya da ‘yan siyasa da masu ruwa da tsaki da kuma al’umma baki ɗaya musamman ‘ya’yan jam’iyyar ta APC dangane da fafatawa a zaɓen dumu-dumu da suka yi daga farko har ƙarshe.

Ya cigaba da bayyana, “dole ku riƙa nuna gaskiya da adalci a harkokinku yanzu da kuka dau rantsuwar kasancewa shugabanni nagari musamman a harkoki da suka shafi dukiyar al’ummarku na karkara. 

“A nan zan ce Ina so in tayaku murnar nasara da kuka samu a matsayin sabbin zaɓaɓɓun shugabannin ƙananan hukumomin mu,” inji shi.

A nasa ɓangaren sakataren gwamnatin jihar Barista Muhammad Ubandoma Aliyu ya bayyana cewa baiyi mamakin nasarar da jam’iyyar APC tayi a zaɓukan ba kasancewa jam’iyyar ta jama’a ce mai kuma farin jini kana ya yaba wa gwamna Sule dangane da talllafawa hukumar zaben jihar yadda ya kamata da hakan ya bada damar cimma nasarar shirya ingantaccen zaɓen da sauransu.

Wakilinmu dai ya ruwaito cewa waɗanda aka rantsar da sun a matsayin sabbin shugabannin duka ƙananan hukumomin 13 a jihar a inuwar jam’iyyar APC mai ci a jihar sun haɗa da Hon. Safiyanu Isah Andaha na ƙaramar hukumar Akwanga, Hon. Umar Abubakar ɗan’ Akano-Awe Hon. Jonathan Addra Okuba Radom’s, Barr. Abubakar Aliyu Madaki – Karu, Hon. Adamu Aboki Usman-Keana, Hon. Dr Idris Ahmed Danmagani – Keffi.

Sauran su ne Hon. Agbawu Mek Agbawu-Kokona, Hon. Mohammed Arabo Haliru-Lafia, Hon Mohammed Hassan Ahmed-Nasarawa, Barr Iliya Ibn Aliyu – Nassarawa Eggon, Hon Mohammed Isa KK- Obi, sai kuma Hon. Ahmed Baba Yahaya na Toto da Hon. Ezekiel Musa Jagga na Wamba.

A yayin da su kuma wasu jam’iyyun adawa guda biyu da suka fafata a zaɓukan wato jam’iyyar SDP da Zenith-Labour suka lashe kujerun kansiloli 5 da guda 2 daki-daki.

By ukarofi