
Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa, ya ƙaddamar da sabbin tashoshi na hukumar sufuri ta jihar, KTSTA, a ƙananan hukumomin Mashi da Ingawa.
A wajen ƙaddamar da tashoshin da aka yi a manyan ofishin ƙananan hukumomi biyun, Gwamna Raɗɗa ya ce tashoshin za su zama wuraren ajiye motoci da ɗibar fasinjoji daga ƙananan hukumomin biyu har ma da maƙotansu.
Ya ce, faɗaɗa ayyukan KTSTA zuwa wasu sassan jihar na da nufin sauƙaƙa sufuri ga al’umma a yanayin hauhawar farashin man fetur da ake ciki.
Duba da hakan yasa hukumar ke yin rangwame ga matafiya da nufin samar musu da sauƙin farashin sufuri.
Ya kuma yaba wa hukumar KTSTA ƙarƙashin jagorancin Alhaji Haruna Musa Rugoji bisa hoɓɓasan da ya ke yi wajen inganta harkokin hukumar ta fuskoki da dama.
A nasa jawabin, shugaban hukumar, Alhaji Haruna Musa Rugoji, ya ce an tsara sabbin tashoshin ne da manyan wuraren ajiye motoci da ofisoshi.
