Daga GAMBO ISAH
Shugaban ƙaramar hukumar Bama a Jihar Borno, Alhaji Modu Gujja ya yaba wa Gwamna Babagana Umar Zulum kan ayyukan cigaba a jihar Borno da ya kawo tun hawansa karagar mulki.
Modu ya bayyana haka ne yayin zantawarsa da wakilin Blueprint cikin satin nan a Abuja.
Ya ce shirye-shiryen cigaban da gwamnan ya kawo sun haɗa da gina sabbin gidaje tare da sake fasalin Bama da samar da bas-bas ɗin sufuri a Bama, Banki da kuma Gwoza..
Modu, ya ce gwamnan ya kuma gina hanyoyi a dukkanin ƙananan hukumomi 27 da ke faɗin jihar.
Haka zalika Hon. Modu Gujja, ya yaba wa Gwamna Zulum kan yadda yake yaƙi da ta’addanci a jihar tare da tallafa wa jami’an tsaro da kayan aiki da ƙarfafa musu akan ayyukan yaƙi da ta’addanci, inda a cewarsa ya bada gagarumar gudunmuwa wajen yaƙi da ‘yan ta’addar Boko Haram da suka addabi jihar.
Modu Gujja, ya shawarci matasa da su kasance jakadu nagari a yankin, inda ya ce su kasance masu biyayya da bin dokokin ƙasa tare da guje wa sha da tu’ammali da muggan ƙwayoyi.
Shugaban ƙaramar hukumar ta Bama, ya kuma ya shawarci dattawa a yankin don tallafawa shirye-shiryen sake gina, muhallan waɗanda ‘yan ta’addar raba su da gidajensu.
Modu ya kuma shawarci shugabannin ƙananan hukumomin jihar 27 da su cigaba da tallafa wa al’ummarsu kamar yadda Gwamna Zulum ke yi a faɗin jihar.
