Mambobin NYSC sun yi kira da a fara aiwatar da alawus ɗin N77,000

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Mambobin masu yi wa ƙasa hidima sun yi kira ga gwamnatin tarayya da ta aiwatar da alƙawarin bayar da alawus na Naira 77,000 domin rage wahalhalun tattalin arzikin da ake ciki.

‘Yan ƙungiyar sun yi amfani da kafafen sada zumunta na zamani don bayyana damuwarsu a ranar Laraba.

Sun ce duk da amincewar gwamnatin tarayya na sabon mafi ƙarancin albashi a watan Yulin 2024, mambobin ƙungiyar na ci gaba da karɓar tsohon alawus na N33,000.

A cewarsu, tsohon alawus ɗin ya daina ɗorewa saboda yawan sufuri, ciyarwa, da sauran kuɗaɗen NYSC na yau da kullum.

Jawabin na Tuwita ya ce: “Bayan watanni 3, Gwamnatin Tarayya ta yi imanin cewa N33k ya isa ‘yan NYSC su tsira,” in ji @NoorAjuwon.

“Ta yaya za mu maida hankali kan aikinmu na farko da N33k a cikin wannan halin da ake ciki na tattalin arziki?” ya yi tambaya @Arbdoolbasid_Jr.

“Tsarin sufuri: @Eze_na_ujari yana kashe Naira 5,000 wajen safara da kuma Naira 2,000 wajen bayar da gudunmuwar ma’aikatan ci gaban al’umma (CDS) wanda ya bar masa N26,000 daga cikin alawus-alawus ɗin N33,000.

“Matsalar rayuwa: @blazzin_225 ta bayyana halin da ake ciki a matsayin “wahala da mugunta” sakamakon munanan gidajen NYSC, gurɓacewar banɗaki da yunwa.

Kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya (NAN) ya rawaito gwamnatin tarayya ta amince da sabon mafi ƙarancin albashin ma’aikata bayan ƙarewar tsohon tsarin albashin a watan Afrilu. Ana sa ran za a miƙa sabon amincewa ga mambobin ƙungiyar.

By ukarofi