
Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gwamnatin jihar Katsina da haɗin-gwiwar gwamnatin tarayya, ta fara gina gidaje guda 350 a wasu ƙananan hukumomin da ƴan ta’adda suka ɗaiɗaita.
Ƙananan hukumomin sun haɗa da Ɗanmusa, Batsari, Ɗandume da kuma Faskari.
Mai taimaka wa gwamnan na musamman kan lamuran ƴan gudun hijira, Alhaji Sa’idu Ibrahim Koguna Jibiya ya bayyana wa manema labarai hakan a Katsina.
Ya ce, tuni gwamnatin Katsina ta biya nata kason yayin da ta ma gwamnatin tarayya na na ƙoƙarin biyan nata domin aikin ginin ya cigaba don a kammala akan lokaci.
Alhaji Sa’idu Ibrahim ya ce, gwamnatin Katsina tana haɗa gwiwa da wasu cibiyoyi na Majalisar Ɗinkin Duniya da ke tallafa wa al’umma domin inganta rayukan mazauna garuruwan da ƴan ta’adda suka addaba.
Ya kuma ce, gwamnatin Dikko Raɗɗa na nata ƙoƙarin tallafa wa jami’an da ta’addanci ya shafa da iyalan su.
“Sun kuwa haɗa da iyalan sojojin da sauran jami’an tsaron da ƴan bindiga suka kashe da waɗanda suka samu raunuka”, inji Koguna.
Haka nan, gwamnati na kai ɗauki a duk lokacin da ƴan bindiga suka kashe ko raunata mutane a waɗannan yankunan da ta’addancin yayi ƙamari a jihar.
