
Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
A zaman da ta yi karo na tara, majalisar zartarwa ƙarƙashin gwamna Dikko Raɗɗa ta amince da kashe Naira 1.5b wajen ɗaukar sabbin jami’an tsaro na cikin gida a jihar.
Kwamishinan tsaro na jihar, Dakta Nasiru Mu’azu Ɗanmusa ya bayyana hakan ga manema labarai bayan kammala taron majalisar zartarwa ta jihar.
Ya ce, za a yi amfani da kuɗin ne wajen horas da jami’an tsaron tare da sama musu kayan da za su gudanar da ayyukan tsaro a ƙananan hukumomi goma da ƴan ta’adda ke yin ta’addanci.
Ɗanmusa ya bayyana sunayen ƙananan hukumomin waɗanda suka haɗa da Dutsinma, kurfi, Charanci, Musawa da Matazu, Malumfashi, Ɗanja, Ƙafur, Bakori da Funtua.
Majalisar Zartarwar ta kuma amince da ware wasu ƙuɗaɗe da adadinsu ya kai N12.5b wajen sayan kayan gwaje-gwaje a asibitin Ahmadi Rimi da ke katsina.
Babban Sakataren Ma’aikatar Kiwon Lafiya, Dakta Ahmed Tijjani ya faɗi haka a wajen taron manema labarai inda da ya ce tuni an fara gina cibiyar gwaje-gwajen.
Ya ce, idan an kammala ginin cibiyar, za ta zama mafi kyau a ƙasashen Afrika ta Yamma.
