
Daga BELLO A. BABAJI
Hukumar bada agaji ta gaggawa, NEMA ta ce ambaliyar Maiduguri ta soma janyewa yayin da mutane suka fara koma wa gidajensu.
Darakta-Janar ta hukumar, Zubaida Umar a lokacin da ta ke bada bayanai game da yanayin al’amarin, ta bayyana cewa, ambaliyar ita ce mafi muni a tarihin Nijeriya kamar yadda ya ke a wata takarda da ta fitar.
Ta ce, kawo yanzu akwai sauran ayyukan da basu kammala ba inda za su cigaba da kula da bada bayanai game da halin da ake ciki.
Ta kuma ce, gwamnatin jihar ta samar da sansani guda takwas ga waɗanda iftila’in ya afka wa da adadisu ya kai mutum 400,000.
Daraktar ta ƙara de cewa, mutanen suna samun taimako daga hukumomin tsaron da ƙungiyoyin al’umma da kuma mutanen kirki na jihar.
Har’ilayau, ta ce NEMA ta aika da manyan motoci guda uku masu ɗauke da ruwan wasu sinadarai da za a fisa a birnin don kare yaɗuwar cutuka da ke da alaƙa da ruwa.
