Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gwamna Dikko Raɗɗa ya sanar da haka a wajen bikin kammala samun horo ga sabbin jami’an tsaro na CWC da ya gudana a makarantar samar da horo na Civil Defence a Katsina.
Ya bayyana cewa samar da wannan karin jami’an tsaron,ya zuwa yanzu kananan hukumomi 20 cikin 34 suke yan CWC ya yankunan sa.
Haka kuma malam Dikko Raɗɗa ya ce samar ƙarin waɗannan jami’an tsaron ya nuna ƙudirin gwamnatin sa na maido da zaman lafiya a faɗin jihar.
Gwamnan ya ƙara da cewa dama tun farko yana mai tabbacin, gwamnatin sa na da niyar kawo ƙarshen ta’addanci a jihar,kamar yadda ya yi alƙawari a lokacin da yake yaƙin neman zaɓe.
Ya bayyana cewa za a tura sabon jami’an tsaron su ɗari ƙananan hukumomin Dutsinma da kankiya,”Dutsinma ta yi iyaka da Safana, Ɗanmusa da Matazu inda ta’addanci ya ta’azzara,”inji Dikko.
Gwamnan ya ƙara nanata cewa gwamnatin sa ba za ta yi sulhu da ‘yan bindiga ba” amma tana maraba da duk wani mataki na kawo zaman lafiya,”a cewar gwamnan.
Ya ce tsarin gwamnatin Katsina shine ta bar al’umma a ƙananan hukumomin da rashin tsaro yayi ƙamari dukkan gudanar da zaman sulhu da yan bindiga a yankunan su.
“Rawar da gwamnati ke takawa shine taimakawa wajen shirin samar da zaman lafiya da tabbatar da doka da oda a yankin da ke fama da rashin tsaro a jihar,”Inji malam Dikko.
Gwamnan ya bayyana nasarar da aka samu sakamakon zaman sulhu da ya ya ce watanni 8 kenan ƙaramar hukumar Jibiya ke zaune lafiya,haka kuma ƙaramar hukumar Batsari sun kai watanni bakwai suna zaune lafiya a cewar sa.
“Su ma sauran ƙananan hukumomin da su kai ta fama da ta’addanci a jihar sun fara shaƙar iskar zaman lafiya,”Inji Dikko Raɗɗa.
Ya ce bikin yaye jami’an tsaron CWC na yau ya nuna jajircewar gwamnatin sa wajen yaƙar ta’addanci a duk inda yake a faɗin jihar.
Malam Dikko ya gargaɗi yan bindiga da su guji komawa aikata ta’addanci domin a cewar sa gwamnati za ta sa wando ƙafa ɗaya da duk masu aikata laifi a jihar.
Ya yaba wa jami’an sojin sama da na ƙasa da jami’an yan sanda bisa haɗin kan da suka ba gwamnatin Katsina wajen yaƙar ta’addanci a jihar.
Haka ma gwamnan ya yabawa sarakunan gargajiya da malaman addini bisa tasu gudunmawa da suka bada wajen samar da tsaro a jihar.
Kwamandan CWC a jihar Manjo Janaral Junaidu Bindawa ya bayyana cewa gwamnati ba ta ɗauki jami’an tsaro na CWC domin su kawo matsala ga al’umma ba sai don su magance matsalar.
Ya ce a koda yaushe jami’an tsaron na aiki kafaɗa kafaɗa da sauran jami’an tsaro domin tabbatar da tsaro a yankunan da ke fama da hare haren yan bindiga.
shekara biyu kenan da kafa rundunar jami’an tsaro na CWC.
