Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Hanyar za ta tashi daga Marabar kanya, Fako, Gidan Garba zuwa Dutsen Bori da Tamarke a waɗannan ƙananan hukumomin.
Ɗan majalisa mai wakiltar ƙaramar hukumar Ƙafur Hon. Sha’aibu Wakili ya gabatar da ƙudirin, inda ya nemi abokan aikin shi a zauren majalisar da su goya ma shi baya a samu amincewar ɓangaren zartarwa.
Duk dai a zaman majalisar dokokin, kwamitin kula da harkokin addini ya gabatar da rahoto akan yadda aka gudanar da aikin Hajji na shekara ta 2025.
Kwamitin ƙarƙashin jagorancin Hon Umar Ali Bindawa ya bada da shawarwari ga ɓangaren zartarwa, wanda suka shafi hukumar jin daɗin Alhazai ta jihar.
Hon Bindawa, ya bada shawara ga hukumar Aikin Hajji ta ƙasa, ta sahalewa hukumomin jin daɗin alhazai na jihohi, da su rinƙa tafiyar da sashin kula da lafiyar maniyyatan na jihohin su domin samun sauƙin kulawa.
Shugaban kwamitin majalisar a rahoton da ya bukaci ɓangaren gwamnati da ta yi biyayya ga dokar da ta kafa hukumar ɓangaren naɗi da tura ma’aikata a manyan guraban muƙaman hukumar.
Bayan tattaunawa a kan ƙudirorin, mataimakin kakakin majalisar ya buƙaci akawun majalisar da ya turawa ɓangaren zartarwa domin aiwatar wa.
