Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Raɗɗa, ya amince da sakin sama da Naira biliyan 21 domin biyan giratutu na ritaya da waɗanda suka rasu na Jihar, ƙananan hukumomi da hukumar Ilimi ta ƙananan hukumomi (LEA) a jihar.
A wata takardar sanar wa ɗauke da sa hannun kwamishinan yaɗa labarai da al’adu Dr Salisu Bala Zango ya ce shugaban ma’aikatan jihar, Alhaji Falalu Bawale ya sanar da haka a ofishinsa yayin taron farko na kwamitin da gwamnatin jihar ta kafa domin tsara da shirya yadda za a raba kuɗaɗen.
A cewar shugaban ma’aikatan jihar, kuɗaɗen an tanade su ne domin share dukkan basussukan alawus-alawus na ritaya da na mutuwa daga Satumba, 2023 zuwa Oktoba, 2025.
Bawale ya ƙara da cewa amincewar na da nufin kawar da tarin basussuka tare da inganta walwalar ma’aikatan da suka yi ritaya da iyalan ma’aikatan da suka rasu.
Shugaban ma’aikatan jihar ya kuma bayyana cewa Naira biliyan 7.7 da aka amince da su domin biyan giratuti na ritaya da mutuwa ga tsoffin ma’aikatan gwamnatin jihar za a biya su sau ɗaya tak (one-off) a cikin wannan watan Disamba, 2025.
Yayin da sama da Naira biliyan 14 da aka amince da su domin tsoffin ma’aikatan ƙananan hukumomi da hukumar Ilimi ta ƙananan hukumomi za a biya su a sassa cikin tsawon watanni huɗu, daga Disamba, 2025 zuwa Maris, 2026.
Tun da farko Gwamna Raɗɗa ya riga ya amince da sakin sama da Naira biliyan 23 inda aka biya basussukan gratuity na mutuwa da ritaya daga Janairu, 2019 zuwa Agusta, 2023.
