
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Shugaba Bola Tinubu ya gabatar da Kasafin kuɗin shekarar 2026 na jimillar Naira tiriliyan 58.18.
An gabatar da kasafin ne zaman haɗaka na majalisun Dattawa da Wakilai tun a ranar Alhamis, 12 ga watan Disamba, 2025 wanda jagororin majalisun kamar Shugaban na dattawa Godswill Akpabio da Kakakin na wakilai, Tajudeen Abbas da kuma shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa suka halarta.
Da yake gabatar da jawabi yayin gabatar da kasafin, Shugaba Tinubu ya bayyana hakan a matsayin ‘lokaci na bayyana nasarar zangon gyare-gyaren Nijeriya’.
Ya kuma yi tsokaci akan raɗaɗin da ƴan Nijeriya suek fuskanta sakamakon sauye-sauyen tattali da gwamnatinsa ta kawo, inda ya ce hakan ba zai tafi a banza ba.
Ya ƙara da cewa, matakin tattalin arziƙin Nijeriya (GDP) ya ƙaru da kaso 3.98 a zango na uku na 2025 tare da samun saukar hauhawar farashi akai-akai har sau takwas, lamarin da ya kai an samu kaso 14.45 zuwa watan Nuwamba, 2025.
Haka kuma, ya ce an samu ƙarin samar da wadataccen mai, kuɗin shiga mai gwaɓi na ɓangaren da ba mai ba da kuma ƙarfafa wa masu zuba jari.
A ƙarƙashin abin da ƙiyasta, an ware tiriliyan ₦34.33 a ƙiyasi, inda kuma jimillar kashe-kashe ta kai tiriliyan ₦58.18 trillion, ciki har da tiriliyan ₦15.52 na warware basusuka.
Fannonin da aka ware musu kuɗaɗen kasafin sun haɗa da tsaro, wanda shi ne ya samu kaso mafi girma na tiriliyan ₦5.41 sai ₦3.56 na ababen more rayuwa, sai ilimi ma tiriliyan ₦3.52 da kuma lafiya da ya samu tiriliyan ₦2.48.
