Majalisar Dattawa ta tabbatar da Mohammed da Eyesan a matsayin jagororin NMDPRA da NUPRC

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Majalisar Dattawa ta tabbatar da naɗin Oritsemeyiwa Eyesan a matsayin sabon shugaban Hukumar Gudanarwar Man Fetur na Nijeriya (NUPRC).

Haka kuma, ta tabbatar da Sa’idu Mohammed a matsayin shugaban Hukumar Kula Lamuran Man Fetur na Ƙasa (NMDPRA).

Hakan na zuwa ne bayan da kwamitin haɗaka ƙarƙashin jagorancin Sanata Abdulrahman Kawu ya gabatar na rahotonsa na nazari akan mutane biyun.

A ranar Laraba, Farouk Ahmed ya yi murabus a muƙamin shugaban NMDPRA yayin Shugaban rukunin kamfanonin Ɗangote, Alhaji Aliko Ɗangote ya ɗora zargin rashawa akansa.

Kakakin Shugaban Ƙasa Bayo Onanuga ya sanar da cewa Gbenga Komolafe ya sauka daga shugabancin NUPRC.

Daga lokacin ne Shugaba Bola Tinubu ya aike da sunayen Mohammed da Eyesan ga majalisar domin ta tantance su a muƙaman da waɗancan mutanen biyu suka bari.

Akan zargin tsohon shugaban NMDPRA da hannun a rashawa, Ɗangote ya yi ƙorafinsa ga Hukumar Yaƙi da Rashawa da Wasu Manyan Laifuka (ICPC) da ta yi bincike akansa.

Ɗangote ya zargi Farouk Ahmed da kashe jimillar Dala miliyan 5 akan karatun sakandare na ƴaƴansa su huɗu a makarantun ƙasar Switzerland.

By Babaji