Daga ABDULLAHI Muhammad a katsina
A zaman majalisar karo na takwas ƙarƙashin jagorancin Gwamna Dikko Raɗɗa ta amincewa da ɗaukar ƙarin matasa 361 a kashi na biyu na shirin koyon noma da kiwo na zamani na Dikko Raɗɗa Agric Training and Empowerment Program a cibiyar horaswa ta Makera Songhai da ke Dutsin-ma.
Shirin horaswar zai mayar da hankali kan bunƙasa ƙwarewar matasa a tsarin noma na zamani da ya haɗa fannoni daban-daban, ciki har da noman amfanin gona, kiwo, kiwon kifi, sarrafa kayayyakin noma da shi kanshi kasuwancin noma.
Marigayi Umaru Musa Yar’adua ya fara kirkiro wannan shiri a lokacin yana gwamnan jihar Katsina.
Haka Kuma gwamnatin ta amince da karɓa tare da yaɗa sakamakon binciken gidaje (General Household Survey – GHS) na shekarar 2025. Wannan amincewar na da nufin aiwatar da tsarin bunƙasa karkara, tare da amfani da bayanan bincike a matsayin abin dogaro ga jihar domin magance ƙarancin ingantattun bayanai da ke kawo cikas ga tsare-tsaren gwamnati, wasu ma’aikatu, hukumomi da kuma abokan hulɗar ci gaba da ke zuwa jihar.
Majalisar zartarwa ta Kuma bayar da kwangilar kammala cibiyar harba ruwa ta zamani da sauran kayayyaki a madatsar ruwa da ke Ajiwa. Wannan aiki zai taimaka wajen dawo da aikin madatsar ruwan tare da ƙara yawan samar da ruwa ga birnin Katsina da garuruwan dake kewaye da ita.
Ta Kuma ƙara alawus ɗin tallafin karatu (Scholarship) da kashi 100 ga ɗaliban jihar da ke karatu a manyan makarantu daban-daban a faɗin ƙasar nan. Wannan mataki na daga cikin ƙoƙarin gwamnati na faɗaɗa damar samun ilimi, rage wa ɗalibai nauyin kuɗaɗen karatu da kuma ƙarfafa ƙwazon karatu.
Gwamnati ta amince da bayar da kwangilar cigaba da aikin sabon filin wasanni na garin Charanchi, wanda ya haɗa da gina filin ƙwallon ƙafa na zamani, shimfiɗa ciyawa ta zamani, babban ɗakin wasanni na bai daya da sauran ayyuka. Idan aka kammala aikin, filin wasan zai zama ingantaccen cibiyar wasanni ta zamani.
Duk dai a zaman, majalisar ta bayar da kwangilar saka ciyawa ta zamani mai inganci (FIFA Quality Pro-Generation Hybrid Synthetic Grass) a filayen wasanni na Malumfashi da Funtua. Aikin na da nufin mayar da filayen wasan zuwa matakin ƙasa da ƙasa, tare da ƙarfafa harkokin wasanni da bunƙasa ruhin wasanni a tsakanin matasan jihar.
Ta umurce ƙananan humomi na jihar su bayar da tallafin karatun jami’a na musamman ga ɗalibai 50 mafi hazaƙa daga kowace ƙaramar hukuma 34 ta jihar.
Tallafin zai haɗa da biyan kuɗin makaranta gaba ɗaya tare da ba su alawus na shekara-shekara. Shirin na da nufin bai wa haziƙan ɗaliban jihar damar ci gaba da karatu ba tare da tangarɗa ta rashin kuɗi ba.
