Gwamnatin Katsina za ta gina rijiyoyin burtsatse 3,000

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Kwamishinan yaɗa labarai Dr Salisu Bala Zango ya faɗawa manema labarai haka da ya ke bayani kan sakamakon zaman majalisar zartarwa karo na huɗu wanda aka gudanar a zauren majalisa wanda gwamna Dikko Raɗɗa ya jagoranta.

A cewarsa, majalisar ta tattauna sosai kan manufofi da ayyukan da za su inganta rayuwar jama’a, ƙarfafa masu rauni, da tabbatar da ɗorewar samun muhimman ayyuka a faɗin Jihar Katsina a cewar kwamishinan.

Kwamishinar Harkokin Mata, Hajiya Aisha Aminu Malumfashi, ta bayyana cewa majalisar ta amince a fara ɗaukan matakan da suka dace domin aiwatar da manufar ƙasa ta ƙarfafa tattalin arziƙin mata a cikin jihar.

Ta ce manufar za ta ƙarfafa shigar mata a fannoni daban-daban na tattalin arziƙi.

“Wannan manufa za ta tabbatar da cewa mata ba a bar su a baya ba a bunƙasar tattalin arziƙin Nijeriya, ta hanyar ƙarfafa shigarsu a matsayin ma’aikata, ‘yan kasuwa da shugabanni a fannoni daban-daban,” in ji ta.

Ta ƙara da cewa shirin zai rage giɓin da ke tsakanin maza da mata tare da ƙarfafa ci gaban tattalin arziƙin mata a faɗin jihar.

A nasa jawabin, kwamishinan Noma, Hon. Aliyu Lawal Shargalle, ya ce majalisar ta kuma amince da gina rijiyoyin burtsatse guda 3,000 a shiyyoyin sanata uku domin tallafa wa aikin gona.

Ya bayyana shirin a matsayin wata muhimmiyar dabara don inganta ban ruwa da ƙara yawan amfanin gona a jihar.

“Shirin na daga cikin ƙoƙarin gwamnati na bunƙasa noma ta hanyar samar wa manoma sauƙin samun ruwa da sauran muhimman kayayyaki da ayyuka,” in ji kwamishinan.

Ya ƙara da cewa aikin zai fi amfani ga ƙananan manoma, da haɓaka noman rani, da kuma ƙarfafa wadatar abinci a jihar.

Shi ma Babban Sakataren ma’aikatar albarkatun ruwa ta Jihar Katsina, Malam Dasuki Abubakar, ya ce majalisar ta amince da sayo sinadarai na tsarkake ruwa domin rufe zangon ƙarshe na shekarar 2025 da wani ɓangare na farkon zangon 2026.

Ya ce hakan na da muhimmanci domin ci gaba da samar da ruwan sha mai tsafta da aminci ga al’umma.

“Za a rarraba sinadaran zuwa matatun ruwa na jihar domin tabbatar da ci gaba da samar da ruwan sha mai tsafta ga mazauna babban birnin jihar da sauran al’ummomi,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa matakin zai hana tangarɗa a ayyukan tace ruwa tare da tallafa wa ƙoƙarin gwamnati na inganta lafiyar jama’a da tsafta.

By ukarofi