Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gwamnatin Jihar Katsina ta bayyana tsarinta na kasafin kuɗin shekarar 2026, inda ta ware biliyoyin nairori domin bunƙasa harkar tsaro, ilimi, lafiya, tattalin arziƙi, noma da ababen more rayuwa, a daidai lokacin da take ƙoƙarin aiwatar da ajandar Gwamna Dikko Raɗɗa mai taken “Building Your Future.”
Kwamishinan kasafi da tsare-tsaren tattalin arziƙi, Alhaji Malik Anas, ne ya bayyana haka a taron manema labarai a Katsina , yana mai bayyana kasafin kuɗin a matsayin “na al’umma, wanda aka tsara bayan tattaunawa da al’umma a ɗaukacin unguwanni 361 na jihar.”
Kwamishinan ya ce, gwamnatin jihar ta sake jaddada tsaro a matsayin sahun gaba, yana mai cewar an ware Naira biliyan 1.2 domin muhimman samar da kayan aikin tsaro, Naira miliyan 500 don sayen alburusai a matsayin kuɗin haɗin gwiwa,inda Naira biliyan tara ga asusun ƙananan hukumomi, biliyan 2 daga gwamnatin jiha, Naira miliyan 100 don samar da wuraren kiwo a dajin rugu, Naira miliyan 150 don shirin Climate Peace Hub.
Alhaji Anas ya ce tsarin zai taimaka wajen tabbatar da jihar Katsina ta zama mai tsaro da kwanciyar hankali,
ƙarfafa tattalin arziƙi da tallafa wa marasa ƙarfi.
A ɓangaren bunƙasa tattalin arziƙi kuwa, Anas ya ce gwamnatin ta ware Naira biliyan 10 don tallafa wa ƙanana da matsakaitan sana’o’i (MSMEs), sai Naira biliyan 3.33 don Shirin ƙarfafa ‘yan kasuwa masu digiri, Naira biliyan 10 don Shirye-shiryen Zuba Jari na Zamani, Naira biliyan 7.68 don sayen hatsi domin rage raɗaɗin talauci ga marasa galihu, yana mai cewar “shirin na da nufin ƙarfafa sana’o’i da kare marasa ƙarfi daga matsin tattalin arziƙi.”
Kwamishinan ya bayyana cewa ɓangaren ilimi ya samu kaso mai yawa, inda a ka ware Naira biliyan 28 don gina makarantu da horas da malamai, Naira biliyan 17.5 don sabbin makarantun sakandare, Naira biliyan 15 don ayyukan AGILE, Naira biliyan 13.6 don ginawa da gyaran makarantun firamare, da kuma ware sama da Naira biliyan shida don tallafin karatu da rage kuɗin jarabawa.
A fannin lafiya kuma, Anas ya tabbatar da cewar gwamnatin jihar ta ware Naira biliyan 20.5 don gyaran asibitoci, tare da Naira biliyan biyar don sabunta cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko da kuma wasu aikace-aikacen sabis na gaggawa.
Haka kuma, a cewarsa, an ware Naira biliyan ɗaya don tallafa wa rukunin jama’a masu rauni da Naira biliyan 5.26 don shirin nan na ‘Nigeria for Women
A ɓangaren gine-gine da hanyoyi kuwa ya ce gwamnati ta ware Naira biliyan 15 don gyaran hanyoyin birane, Naira biliyan 12.21 don hanyar Kunduru zuwa Kadanya, Naira biliyan 12 don hanyar nan ta Daura Western Bypass, Naira biliyan 15 don sabbin gidajen zama, Naira biliyan 5 don sayen bas-bas 30 masu amfani da tsarin haɗaka (hybrid) na wutar lantarki da amfani da hasken rana.
Kwamishina Anas ya ce “Kasafin kuɗin 2026 na nuna aniyar gwamnati na samar da ci gaba mai ɗorewa da walwalar al’umma, tare da ciyar da ajandar “Building Your Future” gaba.” In ji shi
Anas ya bayyana cewar, gwamnatin Malam Dikko Umar Raɗɗa za ta tabbatar da aiwatar da kasafin Kudin yadda ya kamata domin ganin an samu sakamako a zahiri a rayuwar al’ummar Jihar Katsina.
Ya yi kira ga hukumomin tattara haraji da su tashi tsaye domin cimma adadin da ake sa ran samu a wannan shekara.
