
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Jami’an Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (ICPC) sun kai samame gidan tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai da ke Abuja.
Hakan ya biyo bayan kama shi da aka yi bayan Hukumar Yaƙi da yi wa Tattalin Arzikin Ƙasa Ta’annati (EFCC) ta bayar da belinsa.
Rahotanni sun bayyana yadda jami’an ICPC suka kama El-Rufai bayan da EFCC jim-kaɗan bayan bada belin nasa a ranar Laraba.
A daren Alhamis, Muyiwa Adekeye, mai magana da yawun El-Rufai, ya wallafa a shafukan sada zumunta cewa an kai samame gidan tsohon gwamnan na Aso Drive.
Rahotanni sun bayyana cewa jami’an hukumar sun isa gidan ne domin gudanar da bincike akan wasu batutuwa da ake danganta su da tsohon gwamnan, kodayake ba a fitar da cikakken bayani akan dalilin samamen ba a hukumance.
Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, babu wata sanarwa a rubuce daga bangaren El-Rufai ko wakilansa da ke tsokaci akan al’amarin.
