Gwamnatin Nijeriya ta yi maraba da naɗin Maryam Bukar a matsayin jakadiyar zaman lafiya ta duniya

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

A ranar Litinin ne gwamnatin Shugaba Tinubu ta karɓi baƙuncin fitacciyar mai waƙar baka Maryam Hassan wadda ta yi nasarar zama Jakadiyar zaman lafiya ta Majalisar ɗinkin Duniya.

Mataimakin Shugaban Nijeriya Kashim Shettima ne ya karɓi baƙuncin Jakadiyar da tawagarta a fadar shugaban ƙasa inda ya bayyana farin cikin gwamnati da shirinta na yin aiki da Jakadiyar ‘yar asalin Nijeriya don ƙarfafa zaman lafiya a Nijeriya da ma duniya baki ɗaya.

Da yake jawabi ga tawagar ta Global Adɓocate for Peace ta Majalisar ɗinkin Duniya, Shettima ya bayyana Maryam a matsayin mace mai tsayuwar daka wajen sadaukar da basirarta ga wanzar da zaman lafiya musamman a wata ƙasidarta mai taken ‘Rikici bai da addini’  “wannan ita ce Nijeriyar da muke fata, ni a wurina ma wannan ƙasidar ce bakandamiyar Maryam” inji Shettima

Kazalika, Kashim Shettima ya jaddada tsayin dakar da Maryam ta yi na ganin abubuwa sun  daidaita a mahaifarta wato jahar Borno duk da ƙalubalen da ta fuskanta a matsayin wani abin a yaba.

Mataimaki shugaban ƙasar ya tabbatarwa da Majalisar ɗinkin Duniya goyon bayan  gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu inda ya bayar da tabbacin cewa gwamnatinsu za ta yi duk mai yiwuwa wajen bai wa Maryam da ma sauran matasa goyon baya da tallafa musu.

“Ki kwantar da hankalinki Maryam, ba ke kaɗai ba ce, muna tare da ke, kuma duk wani goyon baya da kike bukata, za mu ba ki shi” inji Shettima.

Tun da farko, shugabar tawagar ta Majalisar ɗinkin Duniya First Global Adɓocate for Peace, wato Maryam ta ce aikinta na farko shi ne ta isar da sakon zaman lafiya a duniya, tare da bugan ƙirjin wajen yin fiye da bayar da shawara a ɓangaren  wanzar da zaman lafiya a ƙasarta Nijeriya a fannin da ta fi ƙwarewa.

By ukarofi