
Daga BELLO A. BABAJI
Gwamnatin Sakkwato ta sanar da shirinta na gina madatsun ruwa guda uku a ƙoƙarinta na taimaka wa ayyukan noman fadama da na rani a jihar don inganta harkar noma.
Mai taimaka wa gwamnan kan harkar tattali, Bashir Achida ya faɗi hakan a yayin wata hira da manema labarai a Abuja, ranar Juma’a.
Ya ce, gwamnatin jihar za ta sayi motocin gona, wato tirakta guda 244 don inganta noman zamani duk don tabbatar da samun isasshen abinci ga kasuwa da al’ummar jihar.
Achida ya bayyana hakan a matsayin wani shiri na inganta al’umma wanda acikinsa akwai kiwon dabbobi da kaji da kuma samar da dalar shinkafa a kowane ɗaya daga cikin shiyyoyi uku na jihar.
Ya ƙara da cewa, kasancewar jihar na ɗaya daga cikin jihohi masu fitar da mafi yawan amfanin gona ya sa ta zama kan gaba wajen samar da albasa da tafarnuwa a Afirka ta Yamma.
Kawo yanzu, gwamnatin ta samu damar sayan iri, taki da kayan aikin gona inda kuma ta na aiki tuƙuru don ganin an kauce wa samun asara kafin nome ababen da za a shuka.
