Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta bayyana shirin soke jarrabawar shiga makarantar sakandare ta ƙasa, wato Common Entrance, tare da ƙaddamar da wata sabuwar hanya ta bai wa kowane ɗalibi lambar shaida ta musamman domin bibiyar tafiyarsa ta karatu tun daga firamare har zuwa mataki na gaba.
Ministan Ilimi na ƙasa, Dakta Tunji Alausa, ne ya bayyana wannan shiri yayin wata ganawa da manema labarai a birnin Legas, inda ya ce manufar wannan sauyi ita ce faɗaɗa damar samun ilimi da kuma tabbatar da ingantaccen tsarin sa ido kan ci gaban ɗalibai a faɗin ƙasar.
A cewarsa, za a daina amfani da tsarin jarrabawar Common Entrance a hankali, inda za a maye gurbinsa da tsarin tantancewa na ci gaba Continuous Assessment, wanda zai riƙa auna ƙwarewar ɗalibi tun daga aji na farko na firamare.
Ya bayyana cewa wannan tsarin zai ba ɗalibi damar ɗaukar sakamakonsa tare da shi ko da ya sauya makaranta daga wuri zuwa wani.
Ministan ya jaddada cewa sabon tsarin zai taimaka wajen magance giɓin da ake samu wajen sauyin ɗalibai daga firamare zuwa sakandare, musamman yadda yawancin yara ke kasa ci gaba da karatu bayan kammala firamare.
Ya bayyana cewa a halin yanzu akwai makarantu na firamare sama da dubu 50 na gwamnati a Nijeriya, tare da ɗalibai fiye da miliyan 23, amma daga cikinsu, sama da miliyan uku kaɗai ne ke samun damar shiga makarantar sakandare ta gwamnati. Wannan, a cewarsa, na nuni da babbar matsalar rashin damar karatu ga yara.
“Tambayar ita ce, ina sauran kusan miliyan 20 ɗin da ba su shiga sakandare ba?” inji shi, yana mai cewa dole ne a ƙara gina makarantu domin ɗaukar yawan ɗaliban.
Alausa ya kuma bayyana cewa gwamnati na shirin ƙaddamar da “Lambar Shaidar ɗalibi” (Learner Identification Number), wadda za ta kasance ta musamman ga kowane yaro tun daga matakin firamare. Wannan lamba za ta kasance tare da ɗalibi a duk inda ya je, kuma za ta taimaka wajen bin diddigin ci gabansa da kuma gano waɗanda suka daina zuwa makaranta.
Ya ƙara da cewa, idan aka lura ɗalibi bai ci gaba zuwa mataki na gaba ba kamar yadda ake tsammani, gwamnati za ta iya gano dalilin hakan cikin sauƙi.
Bugu da ƙari, ministan ya ce ana ƙoƙarin farfaɗo da shirin ciyar da ɗalibai a makarantu, domin ƙara yawan shiga makarantu, yana mai cewa ana duba yiwuwar mayar da shirin ƙarƙashin Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya domin inganta sa ido da gudanarwa.
Wannan shiri na daga cikin manyan sauye-sauyen da gwamnati ke ƙoƙarin aiwatarwa domin bunƙasa harkar ilimi, rage yawan yara da ke barin makaranta, da kuma tabbatar da cewa yara a Nijeriya sun kammala ilimin bai ɗaya cikin nasara.
