Gwamnatin Tarayya ta ƙulla yarjejeniya da Majalisar Birtaniya don bunƙasa masana’antar ƙirƙira a Nijeriya

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Ministar Al’adu, Hannatu Musa Musawa, ta ce takardar yarjejeniyar (MoU) da ta sanya wa hannu da Majalisar Birtaniya, an samar da ita ne don haɓaka harkokin al’adu da ƙirƙira gami da ƙarfafa haɗin-gwiwa da ƙasashen duniya.

A wani saƙo daga ma’aikatar, Musawa ta bayyana hakan ne a yayin ganawa da wakilan majalisar a ranar Laraba, 26 ga watan Fabrairu, a Legas.

Hakan ya biyo bayan haɗewa da Ma’aikatar Walwala ta yi da ta Al’adu da kuma ta Ƙirƙirarren Tattali don bunƙasa harkokin al’adu da tattali a Nijeriya.

A lokacin da ta ke jawabi a taron, Musawa ta ce sabon tsarin abu ne da zai inganta ƙarfin baiwar ƴan Nijeriya da sanya ƙasar zama babban jigo a amfani da harkokin ƙirƙira a duniya.

An dai ƙulla yarjejeniyar ce ta tsawon shekaru uku da kuma bada damar ƙari akan haka, wanda Kwamitin Ayyuka na Haɗaka zai kula da aiwatar da shi kamar yadda aka tsara da cimma manyan manufofinsa.

Ta ce, masana’antun Nijeriya suna da damammaki da dama, wanda haɗaka sakamakon yarjejeniyar za ta taimaka wajen yin amfani da su yadda ya dace.

Daga cikin manyan abubuwan da yarjejeniyar ta ƙunsa akwai inganta al’umma da bada horo, musayar al’adu, haɗin-gwiwa tsakanin ƙasashe, inganta tsare-tsare, tallafa wa cibiyoyi, bincike da dai sauransu.

By Babaji