Gwamnatin Tarayya ta bai wa Ɗangote lasisin samar da man jirgin sama ga kamfanonin sufurin jirage 

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Gwamnatin Tarayya ta sanar da cewa an bai wa Kamfanin Ɗangote izini na zama shi kaɗai mai samar da man jirgin sama, ko Jet A1, ga kamfanonin jiragen sama da ke aiki a ƙasar nan.

Ministan sufurin jiragen sama, Festus Keyamo, ya bayyana hakan  a wata hira da aka watsa a tashar Channels TV ranar Talata, 8 ga watan Oktoba.

A cewar Keyamo, kamfanonin jiragen sama sun amince da Kamfanin Ɗangote mai samar da ganga 650,000 na mai a kowacce rana, a matsayin kaɗai mai samar musu da man jirgin sama, tare da amincewarsa da haɗin kansa.

“Kamfanonin jiragen sama sun yi taro kwanan nan. Da yardata, wannan shawarar daga kamfanonin jiragen sama na Nijeriya ce, cewa ya kamata su sayi Jet A1 daga kamfanin Ɗangote kaɗai.

“Kuna iya ganin cewa jiya muka fara sayen mai da ɗangote da Naira. Duka Naira ne, babu wani ɓangare na dala,” inji Keyamo.

Ya bayyana cewa lokacin ya dace saboda ɗangote da gwamnatin tarayya kwanan nan suka fara aiwatar da yarjejeniyar sayen mai da Naira.

Ya bayyana cewa wannan tsarin zai rage nauyin da aka sanya kan kuɗaɗen ƙasashen waje.

“Farashin ba zai kasance ƙarƙashin tasirin kasuwar duniya ba, ko kuma tasirin hauhawar farashin mai a kasuwar duniya. Zai kasance cikin kuɗin gida don mu san daidai farashinsa. Za mu saya cikin Naira. Ina da tabbacin cewa za mu samu Jet A1 mai rahusa,” inji Keyamo.

By ukarofi