
Daga BELLO A. BABAJI
Gwamnatin Tarayya ta shirya kwamitin ministoci game da ranar ƴancin kai ta 2024.
Kwamitin zai kula ne da shiryawa da tabbatar da zartar da baki ɗaya ayyukan da za a yi na karrama ranar.
Nijeriya, wacce Turai ta bai wa ƴancin-kai a shekarar 1960, za ta cika shekaru 64 da samun hakan a ranar 1 ga watan Oktoba, 2024.
Cikin wata takarda da Daraktan Labarai na ofishin shugaban ma’aikatan Fadar shugaban ƙasar, Segun Imohiosen ya fitar, ta ce shugaban ma’aikatan Fadar (SGF), Sanata Akume shi zai jagoranci kwamitin inda ya ce bikin ƴancin-kan za a gudanar da shi ne la’akari da halin da ƙasa ta ke ciki ba tare da tsauwalawa ba.
Akume ya ce, bikin zai zama fage da za a bayyana ayyukan da gwamnati ta yi na daidaita al’amura musamman kan samar da shirye-shirye da za su taimaka wajen farfaɗo da tattalin arziƙin ƙasa.
