Tsage gaskiya: Shin Yahaya Bello ya je ofishin EFCC kuma ya gana da jami’anta?

Spread the love

Daga BELLO A BABAJI

An samu ruɗani game da batun zuwan tsohon gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello hedikwatar EFCC kan bincike da ake shirin gudanarwa akan sa game da badaƙalar wasu biliyoyin kuɗaɗe.

Yayin da ofishin labarai na tsohon gwamnan ya ce mai gidansa ya amsa gayyatar da hukumar ta yi masa, sai kuma hukumar da ta fitar da sanarwar cewa har yanzu shi ɗin mutum ne da ake nema ruwa a jallo.

Ohiare Michael, wanda shi ne Daraktan Ofishin, ya ce, Yahaya Bello ya amsa gayyatar ne bayan tattaunawa da masana harkar shari’a da abokanan siyasarsa wanda an nuna hotuna da bidiyo na zuwan nasa ofishin hukumar kamar yadda jaridar ‘PRNigeria’ ta wallafa.

Acikin wani hoto, an ga Yahaya Bello da gwamnan Jihar Kogi na yanzu, Usman Ododo da kuma wasu jami’an EFCC biyu a harabar hukumar wanda binciken komfuta ya nuna cewa hoton sabo ne.

Bugu da ƙari, PRNigeria ta ce ta yi sharhin hotunan inda ta gano cewa wani Mista Michael Nzekwe ya na cikin hoton kuma shi ne shugaban ma’aikata na EFCC da Mista Ola Olukoyede. Ɗayan kuma wani babban jami’in EFCC ne wanda aka gan shi ya na tattaunawa da Bello da Ododo a harabar hukumar.

Don haka, la’akari da bincike game da hotunan da jaridar ta yi, hakan ya nuna cewa batun EFCC na cewa Yahaya Bello bai je ofishinta ba, haifar da ruɗani ce acikin al’umma.

By Babaji