Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Hukumar Kula da Kadarori ta Nijeriya ta ce kamfanonin jiragen sama na Arik da Aero na iya zama jiregen dakon kaya na ƙasa.
Babban Daraktan AMCON, Gbenga Alade, ya bayyana haka a ranar Litinin a wani taron tattaunawa da kafafen yaɗa labarai a Legas.
A cewar Alade, duka Arik da Aero ana bin su wasu maƙudan kuɗaɗe da ba za su iya biya ba.
Ya bayyana cewa, an gabatar da ra’ayin mayar da Arik da Aero zuwa ƙarƙashin tsohon ministan sufurin jiragen sama, amma aka ƙi.
“Tsoffin shugabannin AMCON sun gabatar da ra’ayin mayar da Arik da Aero zuwa kamfanin jigilar kayayyaki na ƙasa. Amma tsohon ministan sufurin jiragen sama bai aminta da ra’ayin ba. Za mu sake gabatar da shi saboda wannan shi ne mafi kyawun zaɓi..
Idan dai za a iya tunawa, tsohon ministan sufurin jiragen sama, Hadi Sirika, ci gaban ya haifar da damuwa a tsakanin masu ruwa da tsaki game da tsarin mallakar kamfanin wanda ya bai wa kamfanin jiragen sama na Habasha kashi 49 cikin 100 na hannun jarin kamfanin.
Gwamnatin Tarayya ta samu kashi 5 cikin 100 na hannun jari, yayin da wata ƙungiyar masu zuba jari ta Nijeriya uku ke da kashi 46 cikin 100.
