
Daga BELLO A. BABAJI
Gwamnatin Tarayya ta ce za ta ƙaddamar da tsarin ƙin karɓar tsabar kuɗi (cashless tolling system) a babbar hanyar Abuja zuwa Keffi.
Ministan Ayyuka, Sanata Umaho ya bayyana hakan a ranar Alhamis a lokacin da ya ke ƙaddamar da naɗa kwamitin aikin da kuma ninka hanyar Keffi zuwa Akwanga zuwa Makurdi.
Ya ce tsarin, wani shiri ne ƙarƙashin shirin samar da ci-gaba a manyan titina don samar da sufuri mai sauƙi da inganci acikin al’umma.
Ministan ya kuma yaba wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan ƙoƙarinsa na farfaɗo da tattalin arziƙin Nijeriya tare da fatan kwamitin ya tabbatar da yin aikinsa cikin inganci da nagarta don sauƙaƙe wa al’umma a yayin tafiye-tafiye.
Ya ƙara da cewa, a ƙarƙashin aikin akwai sanya kamarorin tsaro da kuma fiitilun kan hanya da ke amfani da hasken rana don tabbatar da tsaro ga dukiyoyi da rayukan al’umma.
