Gwamnatin Yobe ta rufe wasu kasuwanni uku na wucingadi

Spread the love

Daga MUHAMMAD AL-AMIN a Damaturu

Gwamnatin Jihar Yobe ta sanar da matakin rufe kasuwannin mako guda guda uku na wucin gadi wadanda suka shafi Katarko, Kukareta da Buni Yadi- sakamakon dalilan tsaro, na yaƙi da ƴan ta’adda a jihar.

A wata sanarwar manema labaru daga ofishin Bigediya Janar Ɗahiru Abdulsalam (mai ritaya), mai bai wa Gwamna Mai Mala Buni shawara kan harkokin tsaro, ya ce rufe kasuwannin wani mataki ne na gaggawa domin ƙarfafa ƙoƙarin jami’an tsaro na dawo da zaman lafiya mai ɗorewa tare da inganta zaman lafiya a yankunan da abin ya shafa da kuma jihar baki ɗaya.

“Ko da yake wannan mataki na iya jawo ƙalubale ga al’umma, amma yin hakan ya zamo wajibi, a matsayin wani ɓangaren ɗaukar matakan da suka dace a fannin samar da ingantaccen tsaro tare da samun nasarar yaƙi da ayyukan ƴan ta’adda a halin yanzu,” in ji sanarwar.

Gwamnati ta sake jaddada cewa ta na ci gaba da ƙara ƙaimi wajen ganin cewa matakin kawo sauyi da abubuwan da za su rage tasirin rufe kasuwannin kan rayuwar jama’a.

“Saboda haka, mu na kira ga jama’a da su ci gaba da bayar da haɗin kai, fahimta tare da cikakken goyon baya domin ɗorewar zaman lafiya da tsaro a jihar,” In ji Janar Abdulsalam.

Har wala yau, gwamnatin jihar ta bayyana cewa za a buɗe kasuwannin da aka rufe nan gaba kaɗan, bayan shawo kan matsalolin tsaro.

By ukarofi