Isra’ila da Iran: Tsagaitar wutar fatar baki ne ko zuci?

Spread the love

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA

Dama mun hango haka lamarin yaƙin nan zai ƙarƙare da batun komawa teburin sulhu bayan zubar da jini da kan haɗa da ran waɗanda ba su da hannu na nesa ko kusa a abubuwan da a ke taƙaddama a kan su. Gaskiya mutane musamman ma magoya bayan Iran na yankar shakku su riƙa samun kwarin gwiwa ga labarun da ke fitowa cewa Iran na ragargaza Yahudawa. Duk yaƙi ba ya rasa dabaru da ma farafaganda don ƙarya lagon abokin  gaba ko kuma ƙarfafa gwiwar magoya baya. Ko ma me za mu ce sai mun ɗora wannan batu kan wanda ya fara kai farmaki shi ne azzalumi. Isra’ila ce ta fara kai hare-hare har hakan ya yi sanadiyyar rasa ran wasu kwamandoji ɗan asana ilimin kimiyyar ƙera makamai na Iran. Mun dai gani daga bisani an ba da labarin ɗaya daga kwamandojin da a ke tsammanin ya rasa ran sa, ya bayyana don ƙaryata wannan labari. Kuma abun dubawa ga wannan yaƙi shi ne yayin da a zahiri Amurka ke marawa Isra’ila baya, ita kuma Iran ba ta samun wannan mara baya na zahiri daga ƙawayen ta sai dai daga ɗaiɗaikun mutane da bayan tofin Allah tsine ga Isra’ila sai addu’a makamin bayi da su ke yi. Aƙalla wannan yaƙi ya ƙara nunawa duniya cewa Isra’ila kan yi abun da ta dama kuma ta kwana lafiya ko da ba ƙalau ba. Kazalika yaƙin nan na kwana 12 ya kawar da kan mabiya sunna daga bambancin aƙida da al’ummar Iran waɗanda gwamnatin su da akasarin jama’ar su ke bin shia. Mutan sunna sun yi fatar Iran ta yi nasara kan Isra’ila don yadda Yahudawa ke shiryawa musulunci gadar zare ta kowane ɓangare. Ba kan yaki kaɗai ba Yahudawa kan ƙirƙiro lamuran da kan shagaltar da Musulmi su kaucewa addinin su don bin duniya hayaƙin taɓa! Isra’ila tun 1967 ta raina kasashen Larabawa bayan yaƙin ‘yan kwanaki da ya ba ta galaba a kan su duk da an gano bango ne ya tsage a tsakanin Larabawan. Bayan juyin juya hali a Iran a 1979 sai a ka samu tsama tsakanin Farisawa da ƙasashen yamma hade da ‘yar lelen su Isra’ila. Yadda Iran ƙarƙashin Ayatollah kan bugi ƙirjin za ta shafe Isra’ila daga doron ƙasa da kuma fatawar hukuncin kisa ga Salman Rushidie mai littafin ayoyin shaidan ya jawo ƙasashen maida hankali kan Iran. Ba mai inkarin Isra’ila ba ta da makaman ƙare dangi amma ai ba a magana a kan su amma kullum za ka ji a na ta sharhi kan Iran. Wani abun da ya mayar da hankalin Isra’ila kan Iran shi ne yadda ta ke goyon baya ko taimakawa Hamas a Gaza da Hezbollah a Lebanon. Sharhi ya tabbatar da cewa tun harin da Hamas ta kai kan Isra’ila a ranar 7 ga Oktobar 2023 ya sa Isra’ila ƙasar takobin gamawa da Iran da duk ƙungiyoyin da ta ke da alaƙa da su. Kun ga yadda daya bayan ɗaya ta riƙa kasha shugabannin Hamas da kuma jefa bom kan helkwatar Hezbollah a kudancin Beirut. Ga ma yadda ’yan bindiga su ka mamaye Dmaskar da kawar da shugaba Bashar Al’Asad da ke samun goyon bayan Iran. Kai lamarin bai tsaya nan ba don Isra’ila har Yaman ta shiga kai hari kan mayaƙan Houthi. In mun lura a nan Isra’ila ta ɗauko kamfen ne na karya lagon Iran ta kowane ɓangare. Tambaya a nan shin da gaske Isra’ila ta cimma burin ta na karya Iran? Amsa kai tsaye dai ba ta gama cimma burin ba kamar ta jika kayan wanki ne ba ta wanke tsaf ta shanya ba. In mun fahimci Amurka ta kai hari lokaci daya ta dakata don kar yaƙin ya faɗaɗa zuwa shigowar wasu ƙasashe kamar Rasha da Sin da in ba ta ɓaci ba ba za su shigo ba sai dai matakan bayan fage. Wannan yaƙin na da sarkakiya don ba irin yanda Amurka da Rasha su ka raba goyon bayan su a Sham ba. Lokacin yaƙin nasasar Sham, Amurka ta mara baya ga mayaƙa yayin da Rasha ta mara baya ga gwamnati. Duk harin da a ka kai a kan al’ummar Sham ko Siriya ya ke karewa har zuwa cimma matsayar kawar da Asad wanda Rasha ta taimakawa ya fice daga ƙasar zuwa gudun hijira a Masko. Idan yaƙin Iran da Isra’ila ya ja dogon lokaci za a iya ƙirƙiro ‘yan tawaye da ba mamaki ka ga ƙasashe masu nukiliya sun shiga Iran da yaƙi waɗannan na marawa gwamnati baya waɗancan na marawa ‘yan tawaye baya. Kun ga ai Rasha ko Sin ba za su kai hari kan Amurka kai tsaye ba in ba dai an samu akasin yaƙin duniya na uku ba. Na ga a na batun dan tsohon shugaban Iran Sha Ridha Paɓlawi da a ke race-raɗin shi a ke so ya zo don mulkin Iran bayan samun nasarar kawar da gwamnatin ‘yan juyin juya hali da su ka kawar da ta Sha a 1979.

Yanzu dai za mu duba yadda a ka kai ga cimma yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Isra’ila da Iran.

Bayan hare-hare da Amurka ta kai kan sassan kera nukiliya a Iran, shugaban Amurka Donald Trump ya fito ƙarara ya na buƙatar Iran ɗin ta zabi sulhu don rashin yin hakan zai jawo ƙara kai sabbin hare-hare.

A fili Amurka ta afka wannan yaƙi da Isra’ila ta faro fiye da sunan kwance ɗamarar ƙarfin sojan Iran wajen karya lagon kai hare-hare da makamai masu linzami.

Duk da Iran ta maida martani da kai farmaki cikin Isra’ila amma Trump na cewa sun lalata masana’antun kera makaman ƙare dangi na Iran.

A na ta ɓangaren Iran ta tabbatar da kai hare-haren amma ta nuna sam hakan ba zai dakatar da muradin ta na ƙera makamai ba.

Babu cikakkun bayanan irin illar da hare-haren Iran ke yi a cikin Isra’ila don yadda gwamnatin Firaminista Benjamin Netanyahu ke hana manema labaru ɗauko hotuna da fayafayan bidiyo.

Haƙiƙa Iran na bukatar ɗaukar dabarun diflomasiyya da kuma neman goyon baya na zahiri daga kawayen tad a su ka haɗa da Rasha da Sin.

Saudiyya ta yi Allah wadai da hare-haren da Amurka ta kai cikin Iran da ya biyo bayan na Isra’ila.

Ma’aikatar wajen Saudiyya ta fitar da sanarwar nuna takaicin kai harin da bukatar lallai a dakatar da faɗaɗa yaƙin kuma a ma tsayar da hare-haren.

Kazalika Saudiyya ta buƙaci ƙasashen duniya da ke da ruwa da tsaki su ɗau matakin jan birki ga yaƙin da samar da maslaha a siyasance.

Sakataren Majalisar ɗinkin Duniya Antonio Guterres ya caccaki shugaba Trump don ba da umurnin harin kan Iran.

Guterres ya ce, kai farmakin na Amurka ya na da hatsarin gaske don haka ya buƙaci kawo ƙarshen hare-haren.

Duk duniya ta maida hankali kan wannan yaƙin inda alamu ke nuna Iran na taɓukawa duk da ba ta da mataimaka na kai tsaye inda ita kuma Amurka ta fito ƙarara ta na marawa Isra’ila baya har ma ta kai ga Trump yabawa sojojin Isra’ila da matakan zubar da jini ko lalata sassan ƙera makamai na Iran.

AN TSAGAITA BUDE WUTA TSAKANIN ISRA’ILA DA IRAN

An samu tsagaita wuta tsakanin Isra’ila da Iran bayan kwana 12 Isra’ila na kai hare-hare a cikin Iran inda ita ma Iran ke maida martini don kariyar kai.

Shugaban Amurka Donald Trump ya kawo batun tsagaita wutar don haka Isra’ila ya zama mai muhimmanci ta saurara don dama Amurka ke tallafa ma ta da bat a goyon baya marar iyaka.

Abun dubawa shi ne Trump ya bijiro da batun tsagaita wuta bayan umurnin hare-hare da ya ba wa sojojin sa kan sassan ƙera makaman kare dangi na Iran.

Alamu na nuna Trump ba ya sha’awar kawar da gwamnatin Tehran sai dai burin rage kaifin sojan ƙasar da wargaza shirin ta na kera nukiliya.

A na sa ɓangaren Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu na marmarin ture gwamnatin juyin juya hali a Tehran don kafa wata gwamnatin jeka-na-yi-ka.

Haƙiƙa abu ne mai kyau da Iran ta shiga batun na tsagaita wuta maimakon sauraron ɗaiɗaikun magoya bayan ta a wasu ƙasashen waɗanda ke son a cigaba da yaƙi da burin wargaza Isra’ila.

Asarar rayuka a hare-haren Isra’ila ba wani sabon abu ba ne don Isra’ila a fili ba ta mutunta ran kowa waje da na Yahudawa.

Ayyana samun nasara kan Iran da cewa an kifar da shirin ta na nukiliya na samun saɓanin bayanai daga Iran da ke nuna sam ba a yi nasarar mayar da hannun agogo na makaman baya ba.

Ayyana samun nasara kan Iran da Firministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya yi ya saɓa da bayanan da ke fitowa daga Amurka.

Yayin da Netanyahu ke cewa Isra’ila ta mayar da hannun agogon ƙera nukiliya a Iran baya da shekaru, bayanan daga Amurka na nuna hakan na wasu watanni ne.

KAMMALAWA

Gaskiyar Magana hare-haren Amurka da boma-bomai masu shiga ramuka ne su ka yi tasiri kan makerar makaman Iran kuma shugaba Trump ya shaidawa Netanyahu cewa Amurka ba za ta ci gaba da kai hare-hare ba.

Shugaban Iran Masoud Pezeshkian ya ce ƙasar sat a amince da tsagaita wuta kuma za ta dawo teburin tattaunawa.

Pezeshkian ya ba da tabbacin cewa Iran za ta mutunta yarjejeniyar matuƙar ita ma Isra’ila za ta ɗau matakin na gaskiya.

Kazalika Pezeshkian ya ce duk da Iran za ta dawo teburi amma hakan a matsayin ta na kasa mai ‘yanci ba zai hanata ci gaba da bunƙasa nukliya don makamashi ba da lamuran salama.

Ba a yi mamaki da Netanyahu ya ce matuƙar Iran ta dawo aikin ƙera nukiliya, to Isra’ila za ta sake ɗaukar matakan farmaki.

Ya zama mai muhimmanci Iran ta ƙara tsananta ayyukan bayanan sirri na cikin gida don bankaɗo masu leƙen asiri da kan tattara bayanai don miƙawa abokan gaba. Burin kawar da gwamnatin juya juya hali na nan a wajen Isra’ila da masu mara ma ta baya ko ba jima ko bade amma zalunci dai ba ya dauwama duk tsawon zamani.

By ukarofi