Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano
An bayyana cewa ƙananan hukumomin jihar Zamfara 14 za su bajekolin albarkatun da Allah ya hore musu a bikin bajekoli na duniya karo na 46 da aka buɗe a jihar Kano.
Kwamishinan kasuwanci da masana’antu da yawon buɗe ido na jihar Zamfara Hon. AbdulRahman Tunbido Kogunan Maru ne ya bayyana hakan da yake zantawa da ‘yan jarida a yayin buɗe bajekolin a Kano.
Ya ƙara da cewa za su nuna kayan albarkatun su ne domin duniya ta ga irin albarkatun da suke da su musamman a rana ta musamman da za a yi na jihar Zamfara a bajekolin na duniya na jihar Kano.
Ya nuna mutuƙar gamsuwa da shirin da aka yi na bajekolin da aka buɗe karo na 46 na Kano ya ce ana samun kyautatuwar gudanar da bajekolin kowane lokaci domin dama komai ana tafiya ne ana daɗa ingantawa inda aka ga gyara a yi a cigaba, amma gaskiya sun yi abin a yaba suna burin ace kowace jiha a Arewa ta shirya irin wannan domin al’umma su san me suke da shi na albarkatu da me suke bada gudunmawa ta fannin bunƙasa kasuwanci.
Kwamishinan na kasuwanci da masana’antu da yawon buɗe ido na jihar Zamfara Hon. AbdulRahman ya ce lokacin da suka zo Gwamnatin Jihar ƙarƙashin jagorancin Dakta Alhaji Dauda Lawan sun samu kasuwanci ya durƙushe bisa umurnin Gwamna na ganin an haɓaka kasuwanci suka duba masu ƙananan sana’o’i da suke buƙatar tallafi na sana’a irin masu tuyar ƙosai,awara,masa da sauransu suka soma basu tallafi na N50,000 kowane mutum da mutane 25,000 suka amfana.
Ya ƙara da cewa sun sake bada wani tallafin ga yan kasuwa ƙanana da matsakaita da manya wanda ƙananan yan kasuwa an basu tallafi na N150,000 kowanne su 2000 aka baiwa matsakaita N500,000 kowanne Mutum 1000 suma manyan yan kasuwa aka ba kowanne N5,000,000 mutum 60 suka amfana a jimilla sun bada tallafi na Naira Biliyan ɗaya da Naira miliyan 100 a cikin watanni uku da suka wuce.
Hon. Abdulrahman Tunbido Kogunan Maru Kwamishinan kasuwanci da masana’antu da yawon buɗe ido ya ce akwai abubuwa da dama sunanan zuwa domin suna shirin haɗin gwiwa da bankin masana’antu domin samar da bashi mai sauƙi ga yan kasuwa domin inganta masana’antunsu da kamfanoni magana ma ra yi nisa daga nan zuwa farkon shekara mai zuwa mutane za su soma amfana da bashin.
