Gwamnatin Zamfara ta dakatar da shugaban kwalejin kimiyya saboda zargin rashin ɗa’a

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Gwamnatin Jihar Zamfara Ta dakatar da shugaban kwalejin kimiyya da ƙere-ƙere watau Abdu Gusau, Polytechnic Talata Mafara, Dakta Sirajo Abdullahi Shinkafi nan take.

A cikin wata sanarwa da sakataren gwamnatin Jihar, Malam Abubakar Mohammad Nakwada ya sanya wa hannu a ranar Litinin, gwamnatin ta bayyana cewar, rashin ɗa’a da rashin biyayya ga gwamnati sune dalilan dakatarwar ta shi.

“Mai girma, gwamnan Jihar Zamfara, ya amince da dakatarwar nan take ga Dr. Sirajo Abdullahi Shinkafi a matsayin shugaban kwalejin Abdu Gusau, Talata Mafara, saboda rashin ɗa’a da rashin biyayya ga gwamnati,” in ji sanarwar.

Gwamnatin ba ta bayyana takamaiman bayanai game da zarge-zargen da suka haifar da dakatarwar ba amma ta ce shawarar ta biyo bayan sake duba yadda shugaban kwalejin ke gudanar da harkokin makarantar.

Domin hana kawo cikas ga ayyukan ilimi da gudanarwa, sakataren gwamnatin Jihar ya ce an dauki matakai don tabbatar da cewa ba a katse gudanar da karatu a makarantar ba.

Sanarwar ba ta ambaci muƙaddashin shugaban makarantar ba. Duk da haka, ana sa ran mataimakin Dr. Shinkafi zai fara aiki a matsayin muƙaddashi har sai an samu umarni daga ma’aikatar Ilimi mai zurfi.

Abdu Gusau Polytechnic tana ɗaya daga cikin manyan makarantun gaba da sakandare na Zamfara tare da dubban ɗaliban ND da HND.

Bluprint Manhaja ta ruwaito cewa dakatarwar ta zo ne a daidai lokacin da gwamnati ke ci gaba da ƙoƙarin tsaftace harkokin gudanarwa na cibiyoyin gwamnati.

Ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, ƙoƙarin jin ta bakin Dr. Shinkafi bai yi nasara ba.

By ukarofi

Leave a Reply