Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Har yanzu ana cigaba da alhinin rasuwar Babban Hafsan Sojin ƙasan Nijeriya, Taoreed Abiodun Lagbaja, wanda tuni shugaban ƙasa Bola Tinubu ya bayar da umarni a rage ɗagawar da ake wa tutocin Nijeriya a ƙasar.
Janar Lagbaja ne dai mutum na uku da ya rasu a lokacin da yake riƙe da muƙamin babban hafsan sojin ƙasa na Nijeriya.
Lagbaja ne babban hafsan sojin ƙasan Nijeriya 23, kuma ya riƙe muƙamin ne tsakanin Yunin 2023 zuwa Nuwamban 2024, inda ya rasu yana da shekara 56 a duniya bayan fama da jinya.
Baya ga Janar Lagbaja ga wasu manyan hafsoshin sojin ƙasar biyu da suka rasu lokacin da suke riƙe da muƙamin.
Joseph Akahan (Agusta, 1967):
Joseph ne babban hafsan sojin ƙasan Nijeriya na biyu, wanda ya riƙe muƙamin lokacin yana muƙamin Laftanar Kanal, kuma ya yi shekara ɗaya da wata tara, daga Agustan 1966 zuwa Mayun 1968, inda ya rasu yana da shekara 31.
Ya kasance cikin jagororin juyin mulkin 1966, kuma ya rasu ne a hatsarin jirgin sama a lokacin yaƙin basasar Nijeriya.
Shi ne ya jagoranci ƙwato yankin Bonny daga wajen sojojin Biyafara, sannan ya kafa sansanin sojin ruwan Nijeriya.
Laftanar Janar Attahiru (Mayu 21, 2021):
Attahiru shi ne babban hafsan sojin ƙasan Nijeriya 21, wanda ya riƙe muƙamin tsakanin Janairun 2021 zuwa Mayun 2021, bayan ya maye Latfanar Janar Tukur Buratai.
Attahiru ya rasu yana da shekara 54 a hatsarin jirgin sama wanda ya taso daga Abuja zuwa Kaduna.
Attahiru ya karɓi ragamar shugabantar rundunar sojin ƙasa ne a daidai lokacin da rashin tsaro a arewa ya yi ƙamari.
Taoreed Lagbaja (Nuwamba 5, 2024)
Lagbaja wanda tsohon ɗalibi ne a Kwalejin Yaƙin Sojojin Amurka, an ba shi aikin sojan Nijeriya a shekarar 1992.
Kafin a naɗa shi babban hafsa a ranar 19 ga Yuni, 2023, ya yi aiki a matsayin kwamandan runduna a bataliya ta 93 da kuma bataliya ta musamman ta 72.
Ya taka muhimmiyar rawa a ayyukan tsaro na cikin gida da dama, ciki har da Operation ZAKI a jihar Benue, Lafiya Dole a Borno, Udoka a Kudu maso Gabashin Nijeriya, da kuma Operation Forest Sanity a faɗin jihohin Kaduna da Neja.
A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasar, Bayo Onanuga ya fitar, ya tabbatar da cewa shugaban sojojin ya rasu ne a Legas bayan gajeruwar rashin lafiya.
Yanzu haka an maye gurbinsa da abokin karatunsa daga Kwalejin Tsaro, Olufemi Oluyede.
Muƙaddashin hafsan sojin ƙasar ne ya naɗa Oluyede a ranar Larabar da ta gabata, kamar yadda aka tabbatar da cewa Lagbaja ba ya cikin makonni.
