Hajjin 2021: Kano ta ƙaddamar da shirin wayar da kan maniyyata

Daga AISHA ASAS

Hukumar Kula da Walwalar Maniyyata ta Jihar Kano, ta ce ta soma gudanar da shirin wayar da kan maniyyatan jihar a matsayin wani mataki na shirye-shiryen hajjin bana.

Sakataren Hukumar, Alhaji Mohammed Abba Danbatta, ya bayyana wa manema labarai a Kano a cewa, shirin wanda aka ƙaddamar da shi a ranar Asabar da ta gabata zai ci gaba da gudana a cibiyoyin yin rajistar hajjin da ake da su a jihar.

Ya ce manufar shirin shi ne wayar da kan maniyyatan jihar da kuma ilmantar da su kan tsare-tsaren hanjjin bana da kuma yadda ya kamata su tafiyar da kansu a gida Nijeriya da ma can Saudiyya yayin hajji.

Ya ƙara da cewa, shirin zai ci gaba da gudana ne har zuwa lokacin da za a soma jigilar alhazai don aikin hajjin bana. Yana mai cewa, tuni jihar Kano ta soma yi wa maniyyatan jihar allurar rigakafin cutar korona kashi na biyu.

Alhaji Dambatta ya shaida wa HAJJ REPORTERS cewa a can baya ya faɗa wa manema labarai adadi na maniyyatan da za a bari su sauke farali a wannan shekara.

Rahotanni a ƙarshen makon da ya gabata sun nuna Ma’aikatar Lafiya ta Saudiyya ta bada shawarar a lamunce wa maniyyata 60,000 yin hajjin bana kuma daidai da dokokin kariya daga cutar korona. Ta ce maniyyata 15,000 daga wannan adadi su zamana ‘yan Saudiyya ne, sannan ragowar 45,000 su fito daga sauran sassan duniya.