Hana tashin farashin mai ya fi ƙarfina – Dangote

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, wato Alhaji Aliko Dangote, ya bayyana cewa, Nijeriya ba ta da hannu kai tsaye a rikicin Gabas ta Tsakiya, amma duk da haka za ta fuskanci tasirinsa sakamakon yadda tattalin arzikin duniya ya dunƙule wuri guda, don haka hana tashin farashin mai ya fi ƙarfin hamshaƙimin attajirin.

Dangote ya yi wannan bayani ne bayan wata ziyara ta girmamawa da kuma gaisuwar Sallah ga Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, a birnin Legas a ranar Litinin, 23 ga Maris, 2026.

A cewarsa, duniya ta zama tamkar ƙauye ɗaya, don haka duk wani tashin hankali da ya faru a wani yanki zai iya shafar sauran ƙasashe, ko da ba su da hannu kai tsaye a rikicin.

Ya yi gargaɗin cewa rikicin Gabas ta Tsakiya na iya haifar da hauhawar farashin mai a duniya, wanda hakan zai janyo tsadar sufuri, ƙarin hauhawar farashi, da kuma tsanantar rayuwa ga al’ummomin Afirka.

Dangote ya ƙara da cewa idan ba a samu sassaucin rikicin ba, ƙasashe za su fuskanci matsin tattalin arziki, musamman ma a fannin kashe kuɗaɗen tallafi da kuma sauyin kuɗaɗen shiga daga kasuwar mai.

Ya kuma nuna damuwa kan yadda bashin da ƙasashen Afirka ke bin duniya zai iya ƙaruwa, wanda hakan zai rage ƙarfin gwamnatoci wajen tafiyar da harkokin tattalin arziki da tallafa wa jama’a.

A cewarsa, tsadar makamashi na iya shafar kusan kowane fanni na rayuwa, daga ƙananan sana’o’i kamar masu aski zuwa manyan masana’antu da ke dogaro da janareto. “Idan farashin makamashi ya ci gaba da tashi, kowa zai ji tasiri,” inji shi.

Dangote ya kuma lura cewa wasu ƙasashe sun fara ɗaukar matakan rage tasirin matsalar, kamar rage kwanakin aiki, raba amfani da makamashi, da kuma aiki daga gida. Sai dai ya yi gargaɗin cewa irin waɗannan matakai na iya rage yawan aiki da kuma durƙusar da tattalin arziki.

A ƙarshe, Dangote ya buƙaci shugabannin duniya su yi ƙoƙarin rage tashin hankali cikin gaggawa, yana mai cewa al’ummomin Afirka, musamman Nijeriya, suna da matuƙar rauni ga irin waɗannan sauye-sauyen tattalin arziki, domin da dama daga cikinsu suna rayuwa ne da abin da suke samu a kullum.

By ukarofi