Har yanzu ana cigaba da azabtar da mutane a Gaza – Ofishin Jakadancin Palestine

Daga BELLO A. BABAJI

Kimanin kwanaki 419 kenan da mayaƙan haɗin-gwiwa na ƙasashen Amurka da Isra’ila, wato USA-Israeli suke kisan kiyashi tare da ɗaiɗaita dubunnan al’umma a Gaza, kamar yadda ofishin Jakadancin Palestine a Nijeriya ya bayyana.

A cikin wata takarda da Jakadan Palestine a Nijeriya, Abu Shawesh Abdullah ya fitar, ya ce zuwa ranar 27 ga Nuwamba, mutane 44,249 ne aka yi wa kisan gilla yayin da aka raunata 104,746 a Gaza waɗanda mafi yawancin su yara ne da mata, sannan kuma da dama suna tsaka-mai-wuya a buraguzan gine-ginen da aka tarwatsa.

A tare da wasu laifukan yaƙi da suka ci karo da mutumtaka, ta tabbata cewa sojojin Isra’ila na amfani da ƴan Palestine a matsayin masu kare wuraren da suka mamaye daga ƙasar ta Palestine ta hanyar tilasta su, kamar yadda wani rahoton sirri da New York Times ta Amurka ta wallafa.

Ya kuma bayyana cewa, ilimi abu ne mai martaba a wajen al’ummar Palestine inda kaso 95.4 na yara ƴan makaranta ne. Hakan ya fara samun tsaiko ne tun daga shekarar 2007 da kuma lokacin COVID-19 wanda yaƙin na yanzu ya taimaka wa inda ya shafi ɗalibai 625,000 da kuma malamai 22,564 sakamakon tarwatsa makarantu da hare-haren Isra’ila suka yi.

UNICEF ta ruwaito cewa, zuwa watan Oktoba, 2024 an samu hare-hare 64 ga makarantu waɗanda sun ɗaiɗaita Birnin Gaza da Arewacinta, lamari mafi muni da yankin ya samu kansa aciki.

Har’ilayau, zuwa ranar 17 ga watan Nuwamba, kaso 90 na al’ummar yankin sun ɗaiɗaice inda mutane 415,000 suna halin gudun hijira a makarantu 100 dake sassa daban-daban na ƙasar.

Sama da yara miliyan guda ne a Gaza suka watse sakamakon hare-haren waɗanda saboda su ne suka rasa samun kulawa ta fuskar abinci da wasu buƙatun rayuwa.

Hare-haren Isra’ila a Palestine sun yi sanadiyyar rugujewar makarantu da asibitoci da ma’aikatu da wasu kadarorin gwamnati da gidajen al’umma da dubunnan rayuka.