Har yanzu darussan Lissafi da Turanci wajibi ne ga masu neman manyan makarantu, inji Gwamnatin Tarayya

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Gwamnatin Tarayya ta ce har yanzu darussan Lissafi da Turanci suna daga cikin muhimman darussan da ɗaliban sakandare ke buƙata a yayin rubuta a jarabawar kammala karatu a zangon.

Hakan na nufin duk da sabuwar manufar da aka fito da ita kan tsarin karɓar ɗalibai a jami’o’i da wasu manyan makarantu.

A wata sanarwa da Ma’aikatar Ilimi ta fitar a ranar Lahadi, ta ce sabuwar dokar da aka yi ta bai wa jami’o’i sassauci ne wajen shigar da ɗalibai wai za a cire wajabcin rubuta Lissafi ba.

Daraktar yaɗa labarai Misis Boriowo Folasade, fitar da sanarwar yayin da ake yaɗa jita-jitar cewa ɗaliban sashen fasahar zamantakewa ba za su sake buƙatar Lissafi ba wajen neman shiga jami’a.

A ƴan kwanakin nan ne Boriowo ta bayyana cewa sabuwar manufa ta bai wa ɗaliban fasahar zamantakewa damar neman shiga jami’a ko da ba su da ƙwarewa a Lissafi, domin faɗaɗa damar samun ilimi ga dalibai da dama da ke rasa gurbi a kowace shekara.

Ta ce a kowace shekara, fiye da ɗalibai miliyan biyu ne ke rubuta jarabawar JAMB, amma ƙasa da 700,000 ne ke samun gurbin karatu, dalilin da ya sa aka ƙirƙiri sabon tsarin domin rage giɓin.

Saidai hakan ya janyo cece-kuce a tsakanin masana ilimi, duba da ganin zai iya rage ƙoƙarin ɗalibai da kuma sauya ingancin tsarin ilimi a ƙasar.

By Babaji